A dena kira na 'Special One', Mourinho ya bayyana sabon sunan da ya ke so

A dena kira na 'Special One', Mourinho ya bayyana sabon sunan da ya ke so

- Mai kula da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham, Jose Mourinho ya ce baya son tsohon laƙabinsa na 'Special One'

- Ya bayyana cewa daga yanzu yana son a rika masa inkiya da sabon laƙabin 'Experienced One', ma'ana wanda ya ƙware

- Mourinho ya ce duba da tarin shekarun da ya yi ana damawa da shi a harkar kwallon ƙafa, ya samu gogewa da ƙwarewar da ya cancanci sabon laƙabin

Jose Mourinho ya raɗa wa kansa sabon inkiya inda ya bayyana cewa yana son a dena kiransa da lakaɓin 'Special One'.

Jose Mourinho wadda tun shekarar 2004 ake dama wa da shi a gasar Premier ya bayyana cewa laƙabin 'Special One' ta tsufa.

Amma a yanzu ya ce yana son a dinga kiransa da laƙabin 'Experienced One', kamar yadda LIB ta ruwaito.

A dena kira na 'Special One', Mourinho ya bayyana sabon sunan da ya ke so
A dena kira na 'Special One', Mourinho ya bayyana sabon sunan da ya ke so. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

Fitaccen cocin ɗan ƙasar Portugal ya jagoranci Tottenham zuwa Premier League karo na biyu kuma ana yi wa tawagarsa kallon ɗaya daga cikin wadanda za su iya zama zakaru a gasar.

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

Mourinho ya naɗa wa kansa laƙabin 'Special One' a shekarar 2004 a yayin da ya ke tashe sosai a Chelsea.

Tun daga wannan lokacin laƙabin na 'Special One' ke binsa.

Amma a ranar Alhamis 19 ga watan Nuwamban 2020 ya bayyana sabon sunan da ya ke so.

"The Experienced One.' Na goge sosai yanzu, "Mourinho ya bawa manema labarai amsa da suka tambaye shi sunan da ya ke so yanzu.

KU KARANTA: Wike ya ce wani gwamnan PDP daya zai sake fita daga jam'iyyar

"A yanzu galibi ba wani sabon abu da ke faruwa da Ni a ƙwallo da ban taɓa ganin makamancinsa ba.

"Akwai ayyukan da ke buƙatan kuzari kamar ɗan wasan ƙwallo, Ɗan shekara 40 ba zai iya samun kuzari irin ta ɗan shekara 20 ko 30 ba, idan dai kai ba Zlatan Ibrahimovic bane.

"Amma aikin coci ƙwaƙwalwa kawai ka ke buƙata, daɗewa kana aikin yana sa ka koyi darussa kuma ka ƙara goge wa"

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel