Kotu ta yanke wa Olisah Metuh hukuncin daurin shekaru 39 a gidan yari
Olisah Metuh, tsohon kakakin jami'iyyar PDP na kasa, zai shafe tsawon shekaru 39 a gidan yari bayan samunsa da laifin almundahanar kudi.
A ranar Talata, 25 ga watan Fabrairu, alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, Jastis Okon Abang, ya zartar da hukuncin a kan Metuh.
Kafin ya karanta hukuncin da kotun ta yanke, Jastis Abang ya bayyana cewa kotun ta samu Metuh da laifin almundahanar kudi, kamar yadda ake tuhurmarsa.
Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ce ta gurfanar da Metuh bisa zarginsa da almundahanar kudi da yawansu ya kai miliyan N400.
DUBA WANNAN: Abinda yasa NSA Monguno bai halarci taron Buhari da shugabannin hukumomin tsaro ba
Kotun ta yanke wa Metuh hukuncin daurin shekaru 14 a kan tuhuma ta farko da ta biyu ake yi, watau shekara 7 a kan kowacce tuhuma. A tuhuma ta uku da ake yi masa, kotun ta yanke wa Metuh hukuncin daurin shekaru 5, daurin shekaru 7 a kan tuhuma ta hudu da kuma daurin shekaru 6 a kan tuhuma ta biyar da ta shidda, watau shekara uku a kan kowacce tuhuma.
Alkalin kotun ya bayyana cewa Metuh zai shafe shekarun ne a lokaci guda, hakan na nufin cewa zai shafe shekaru 7 ne a gidan yari.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng