Najeriya za ta fara shigo da man fetir daga kasar Nijar, an yi yarjejeniya

Najeriya za ta fara shigo da man fetir daga kasar Nijar, an yi yarjejeniya

- Kurunkus! Najeriya ta shiga yarjejeniya da makwabciyarta, Nijar, na shigo da taceccen man fetur

- Wannan yarjejeniya ya biyo bayan watanni hudu ana tattaunawa tsakanin gwamnatocin biyu

Gwamnatin Najeriya ta shiga sabuwar yarjejeniya da gwamnatin jamhurriyar Nijar na fara shigo da man fetur birnin Zinder.

The Nation ta ruwaito cewa Ministan arzikin man fetur na Najeriya, Temipre Sylva, da Ministan man jamhurriyar Nijar, Mr. Foumakoye Gado, ne suka rattafa hannu kan yarjejeniyar.

"Gwamnatin tarayyar Najeriya da Jamhurriyar Nijar ta rattafa hannu kan yarjejeniyar sufuri da ajiyar arzikin man fetur," ma'aikatar arzikin mai a Najeriya ta bayyana a wani jawabi.

Bayan tattaunawa da aka kasance anayi tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da shugaba Mahamdou Issoufou, na tsawon watanni hudu yanzu, kamfanin NNPC na Najeriya, da Societe Nigerienne De Petrole (SONIDEP), na Nijar sun amince da wannan harkalla.

Matatar man kasar Nijar Soraz dake Zinder, kimanin kilomita 260 da iyakan Najeriya, na da ikon tace kimanin gangan mai 20,000 a rana.

Gaba daya al'ummar kasar Nijar gangar mai 5000 a rana suke bukata, kuma suna da raran ganga 15,000 da suke bukatar sayarwa.

Najeriya za ta fara shigo da man fetir daga kasar Nijar, an yi yarjejeniya
Najeriya za ta fara shigo da man fetir daga kasar Nijar, an yi yarjejeniya Hoto: Presidency
Asali: Twitter

KU KARANTA: ASUU ta gano kadarorin Akawun Gwamnati, kungiya ta bukaci AGF ya yi bayani

A jawabin da Garba Deen Muhammad, hadimin ministan man Najeriya ya saki, yayi bayanin cewa shugaban kamfanin NNPC, Malam Mele Kyari, da Dirakta Janar na SONIDEP, Mr. Alio Toune, ne suka rattafa hannu.

Sun yi hakan ne karkashin jagorancin Ministan man Najeriya,Çhief Timipre Sylva; Ministan man Nijar, Mr. Foumakoye Gado; da sakataren kungiyar kamfanonin man nahiyar Afrika (APPO), Dr Omar Farouk Ibrahim.

Jawabi bayan taron rattafa hannun, Sylva ya bayyana farin cikinsa bisa wannan cigaba, yace haka zai kara dankon zumuncin kasuwancin dake tsakanin kasashen biyu.

KU DUBA: Dogarin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bindige mai jarida ba gaira, ba dalili

A bangare guda, an gano arzikin man fetur mai dimbin yawa a jihar Benue, kuma masana ilimin ma'adinan Najeriya ke jagorantan hakan, shugaban kamfanin man feturin Najeriya NNPC, Mele Jyari ya bayyana haka.

Kyari ya bayyana hakan ne yayin jawabi a taron bude bikin baja kolin kungiyar masu neman arzikin man fetur na Najeriya (NAPE) a ranar Alhamis.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel