Wike ya ce wani gwamnan PDP daya zai sake fita daga jam'iyyar
- Nyesome Wike, gwamnan Jihar Rivers ya gargadi jam'iyyar cewa wani daga cikin gwamnan ta zai sake barin jam'iyyar
- Amma Wike bai bayyana sunan gwamnan da ya ke nufi ba kuma bai sanar da takamaiman ranar da gwamnan zai fita ba
- Wike ya yi ikirarin cewa dama wasu gwamnonin na PDP suna harka da APC cikin dare amma da rana su rika nuna cewa sun 'yan PDP ne
Gwamnan Jihar Rivers Nyesome Wike ya ce wani gwamnan guda daya daga jam'iyyar PDP zai sake ficewa daga jam'iyyar ya koma wata kamar yadda Channels Television ta ruwaito.
"Ina fada maka, akwai wani gwamnan PDP guda daya da zai sake barin jam'iyyar," a cewar Wike yayin hirar da aka yi da shi a shirin Politics Today.
Amma Gwamna Wike bai fadi sunan gwamnan ba da kuma ranar da zai fice daga jam'iyyar ta PDP.
DUBA WANNAN: Hotunan Bashir El-Rufai rike da ƙugun Halima Nwakaego sun janyo masa caccaka
Kamar yadda Umahi ya yi, yana tsammanin shima wannan gwamnan sai bijiro da wani dalili a yayin da i zai fice daga jam'iyyar.
"Maganar dama wadannan gwamnoni ne da sun dade suna yi wa jam'iyya zagon kasa. Suna 'soyayayya' da APC cikin dare amma da rana su fito su ce sun 'yan PDP ne," in ji shi.
Batun yi wa jam'iyya zagon kasa ya dade yana damun Wike amma kamar jam'iyyar ta PDP bata dauki batun da muhimmanci ba kamar yadda ya kamata.
"Matsala ta da jam'iyyar mu shine idan ka fadi gaskiya sai a taso maka, na sha taso da wannan maganar sau da yawa."
Ficewar Umahi daga jam'iyyar ta PDP ya janyo cece-kuce kuma ta rage adadin jihohin da jam'iyyar PDP ke da su a yankin Kudu maso Gabas. Yanzu APC ita ke da jihohin Imo, Ebonyi yayin da APGA ke da Anambra.
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng