Kenneth Gbagi: Abin da ya sa nake neman Gwamnan Jihar Delta a 2023
- Cif Kenneth Gbagi ya yi magana game da siyasar Najeriya da 2023
- Gbagi ya jaddada burinsa na fitowa takarar gwamna a jihar Delta
- A cewar Gbagi, a baya an nemi ya karbi kujerar Minista, amma ya ki
Wani daga cikin manyan jiga-jigan PDP a yankin Neja-Delta, Kenneth Gbagi, ya yi doguwar hira da jaridar This Day, ya kuma yi magana a kan batutuwa iri-iri.
Cif Kenneth Gbagi ya bayyana cewa alakarsa da gwamnan jiharsa, Ifeanyi Okowa, ta na nan lafiya kalau tare da yabon irin ayyukan da gwamnatin mai-ci ta ke yi.
Da aka tambaye shi game da burinsa na hada harkar kasuwancinsa da neman gwamna, sai ya ce ya na da duk abin da ake bukata wajen mulkar al’ummar Delta.
KU KARANTA: Mai garkuwa da mutanen da ke kashe wadanda ya tsare
Gbagi ya ce: “Gwamna ya fada a kunnen Duniya, duk jihar Delta babu wanda ya zuba hannun jari ya ke kasuwanci irina. Ina maganar abubuwan da kowa ya ke gani”
A cewarsa, duk kasuwancin da ya ke yi, bai ci bashin ko sisi daga wani banki ba. Ya ce: “Ko lokacin da na ke Minista, hukumar EFCC ba ta taba taso ni gaba ba.”
“Sau uku ina watsi da tayin rike kujerar Minista.” Amma babban kusan na PDP mai adawa a yau, bai iya bayyana gwamnatocin da su ke nemi yin aiki da shi ba.
“Akwai matasa fiye da 6000 da ke kasuwanci a karkashi na, su na neman na abinci a kullum, saboda haka na san abin da ake bukata a gyara jihar.” Inji Cif Gbagi.
KU KARANTA: An yi ca a kan Gbagi saboda bada umarnin a tube mata a kan N5000
‘Dan siyasar ya bayyana cewa tun daga 1999 zuwa yanzu, babu gwamnan Delta da ya tsaya ya saki jikinsa da shi, ya kuma yi aiki tare da shi kamar Ifeanyi Okowa.
Gbagi ya musanya zargin da ake yi masa na cin zarafin wasu mata, sannan ya yabi James Ibori.
An gayyaci Gbagi ne kan zargin cin zarafin da aka yi wa wasu mata ma'aikatan otel dinsa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng