Na kashe fiye da mutum 50 don sun kasa biyan kudin fansa - Shugaban masu garkuwa

Na kashe fiye da mutum 50 don sun kasa biyan kudin fansa - Shugaban masu garkuwa

- Wani shugaban masu garkuwa da mutane da aka kama mai suna Mohammed Sani ya ce ya kashe fiye da mutum 50 da ya yi garkuwa da su

- Sani ya ce su kan saki wadanda suka biya kudin fansa amma duk wanda bai biya ba kashe shi suke yi

- Sani ya ce wani Yellow Jambros ne mai gidansu kuma shi ke bashi bindigu da khakin sojoji da suke amfani da shi

Daya daga cikin shugabannin kungiyar masu garkuwa da mutane da 'yan sanda suka dade suna nema ruwa a jallo ya amsa cewa ya kashe fiye da mutum 50 saboda sun gaza biyan kudin fansa.

Wanda ake zargin, Muhammad Sani mai shekaru 30 ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 30 ga watan Satumba lokacin da kakakin 'yan sanda Frank Mba ya yi holensa da wasu masu laifin hedkwatan hukumar a Abuja.

DUBA WANNAN: 'Ka gayyato sojojin Chadi su taya mu yaki da Boko Haram' - Zulum ya roki Buhari

Na kashe fiye da mutum 50 don sun kasa biyan kudin fansa - Shugaban masu garkuwa
Na kashe fiye da mutum 50 don sun kasa biyan kudin fansa - Shugaban masu garkuwa. Hoto @Lindaikeji
Asali: Twitter

Sanye da khakin sojoji na bogi, Sani yace ya yi wa Yellow Jambros aiki wanda ya rika bashi bindigu da khakin soji inda ya ce ya yi barnarsa a Kaduna, Katsina, Niger da Zamfara.

Wanda ake zargin ya ce shine kwamandan kungiyar masu garkuwarsu kuma yana da fiye da mutum 120 da ke aiki a karkashinsa.

KU KARANTA: Hotuna: 'Yan sanda sun yi holen 'yan fashi da makami da masu garkuwa a Abuja

Sani ya ce ba zai iya tuna adadin mutanen da ya yi garkuwa da su ba kuma dukkan wanda suka kama kuma bai biya kudin fansa ba sun kashe su.

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi, DCP Mba ya ce sun dade suna neman Sani ruwa a jallo.

"Mohammed Sani shine kwamandan shiyyarsu a wata babban kungiyar masu garkuwa. Yana da fiye da mutum 100 da ke aiki a karkashinsa kuma Sani yana yi wa wani Yellow Jambros aiki ne," in ji Mba.

A wani labairn daban, Rundunar 'yan sandan jihar Delta na neman tsohon karamin ministan ilimi, Kenneth Gbagi ruwa a jallo kan zargin cin zarafin wasu ma'aikatansa a Signatious Hotel.

Tunda farko Legit.ng ta ruwaito cewa Gbagi wanda shine mai otel din, wai ya bada umurnin da tube ma'aikatansa hudu, uku mata da na miji daya a sannan aka dauki hotunansu da bidiyo aka baza a dandalin sada zumunta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel