Cin zarafi: 'Yan sanda na neman tsohon minista Gbagi ruwa a jallo

Cin zarafi: 'Yan sanda na neman tsohon minista Gbagi ruwa a jallo

- 'Yan sanda a jihar Delta na neman karamin ministan ilimi Kenneth Gbagi ruwa a jallo saboda kin amsa gayyatar da aka masa

- An gayyaci Gbagi ne kan zargin cin zarafi da aka yi wa wasu ma'aikatan otel dinsa da aka tube wa kaya aka duke su sannan aka baza hotunan a dandalin sada zumunta

- Da farko Gbagi ya nemi 'yan sandan su masa uzuri ya gama hallarci jana'izar yar uwarsa amma bayan jana'izar ya ki amsa gayyatar

Rundunar 'yan sandan jihar Delta na neman tsohon karamin ministan ilimi, Kenneth Gbagi ruwa a jallo kan zargin cin zarafin wasu ma'aikatansa a Signatious Hotel.

Tunda farko Legit.ng ta ruwaito cewa Gbagi wanda shine mai otel din, wai ya bada umurnin da tube ma'aikatansa hudu, hudu mata da na miji daya a sannan aka dauki hotunansu da bidiyo aka baza a dandalin sada zumunta.

'Yan sanda na neman tsohon minista Gbagi ruwa a jallo
'Yan sanda na neman tsohon minista Gbagi ruwa a jallo. Hoto @TheGuardianNigeria
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An sace shugaban karamar hukuma a hanyarsa ta zuwa gona a Kaduna

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce ta bada sanarwar nemansa ruwa a jallo ne domin ta aike masa ta gayyata a kan zargin amma ya ki ya amsa gayyatar.

Sanarwar neman tsohon ministan na cikin wani sako da rundunar ta fitar ne mai dauke da sa hannun kakakin rundunar na jihar, DSP Onome Onovwakpoyeya da ya bawa The Punch a ranar Laraba a Asaba babban birnin jihar.

Wani sashi na sanarwar ya ce, "Kwamishinan 'yan sanda ta hannun DPO na Warri da Ebrumede a ranar 25 ga watan Satumban 2020 ya gayyaci Olorogun Kenneth Gbagi domin amsa tambayoyi game da zargin cin zarafin wasu ma'aikatansa da aka tube kuma aka yi wa duka.

KU KARANTA: Jawabin rabuwar Najeriya: Dattawan Arewa sun gargadi mataimakin shugaban kasa Osinbajo

"Kenneth Ggabi ya kira sau da yawa ya bada uzurin cewa zai hallarci jana'izar 'yar uwarsa da za ayi a ranar Juma'a 25 ga watan Satumban 2020 ya nemi a bashi lokaci ya gama sai ya zo hedkwatan 'yan sanda na jihar a ranar Litinin 28 ga watan Satumba kuma aka amince masa da hakan.

"A ranar Litinin 28 ga watan Satumba Kenneth Gbagi ya kira kwamishinan 'yan sanda ya sanar da shi cewa yana da shar'a a kotu amma ya yi alkawarin zuwa hedkwatan 'yan sandan karfe 3 na rana kuma bai zo ba.

"A ranar kwamishinan 'yan sandan ya kira shi misalin karfe 5 na yamma ya ce yana hanyar zuwa hedkwatan 'yan sandan amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai isa ba sai dai ya tafi kafafen watsa labarai yana neman cin zarafin kwamishinan da rundunar 'yan sanda saboda binciken da ta ke yi.

"Tunda ya ki cika alkawarin da ya yi, Rundunar 'yan sanda ta jihar Delta ba ta da zabi da ya wuce ta bada sanarwar nemansa ruwa a jallo."

Ana kira ga duk wanda ke da bayanan da za su taimaka wa hukumar kama shi su tuntubi rundunar.

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata 29 ga watan Satumban ya kaddamar da aikin layin dogo na takpe-Ajaokuta-Agbor-Warri ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo mai nuna bidiyo da sauti.

An yi bikin ne a tashan jirgin kasa na Agbo inda aka saka wa tashar sunan tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel