An huro wa tsohon minista wuta kan zarginsa da bada umurnin yi wa ma'aikatansa zigidir saboda N5,000

An huro wa tsohon minista wuta kan zarginsa da bada umurnin yi wa ma'aikatansa zigidir saboda N5,000

- Kungiyoyin kare hakkin bil-adama, lauyoyi da sauran mutane sun bayyana rashin amincewarsu kan tube wasu ma'aikatan otel da aka ce an yi saboda zargin satar N5,000 a Delta

- Ana zargin tsohon karamin ministan ilimi, Kenneth Gbagi wanda shine ya mallaki otel din ya bada umurnin a tube ma'aikatan kafin mika su hannun 'yan sanda

- A martanin da ya yi, Gbagi ya ce ya mika gudanar da ayyukan harkokin otel din ga wasu mutane daban kuma ya yi mamakin jin labarin inda ya ce zai yi bincike

Mutane a ranar Talata sun nuna bacin ransu bisa zargin cin zarafin wasu ma'aikatan wani Otel mai suna Signatious Hotel da ke Warri a jihar Delta da mahukunta otel din suka yi.

Ana zargin cewa shugaban hotel din kuma tsohon karamin ministan ilmi, Mr Kenneth Gbagi ya bada umurnin a yi wa ma'aikatansa hudu zindir - uku mata daya na miji kan zargin sun saci kudi.

An dauki bidiyo da hotunansu kuma wasu daga cikin hotunan sun fito a dandalin sada zumunta kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Tsohon minista ya saka an yi wa ma'aikatan otel zigidir saboda N5,000
Tsohon minista ya saka an yi wa ma'aikatan otel zigidir saboda N5,000. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Fitar da bidiyon lalata na budurwa ya saka ango ya fasa aurenta a Sokoto

Masu kare hakkin bil-adama da masu amfani da dandalin sada zumunta sunyi tir da abinda ya faru sun bukaci kwamishinan 'yan sandan jihar, Hafiz Inuwa ya yi bincike a kuma hukunta masu laifi.

Wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama sun fita titi sunyi zanga-zanga a Asaba don nuna kin amincewa da cin zarafin da aka yi wa ma'aikatan otel din masu suna Gloria Oguzie, Victor Ephraim, Rosslyn Okiemute da Precious Achibong.

Shugaban masu zanga-zangar kuma direktan oung Nigerian Right Organisation, Victor Ojei, ya yi ikirarin cewa mai otel din ne yasa 'yan sanda suka kama ma'aikatan saboda N5,000.

Ya yi ikirarin cewa an tube matan da na mijin a gaban 'yan sanda da aka kira su tafi da su.

Ya ce, "Mahukunta otel din sun tsare na miji daya da mata uku, sun tube su a dakin otel, sun dauki hotuna da bidiyonsu.

"Ranar Juma'a da ta gabata, mahukunta otel din sun tube matan sun dauki hotuna da bidiyonsu a gaban 'yan sanda da bindigu. An kuma cire kudade daga asusun bankin su kafin 'yan sanda suka tafi da su.

"Kamata ya yi 'yan sanda su rika kare mutane ba a hada baki da su wurin cin zarafinsu ba. Ko ma dai da gaske sunyi sata ba haka ya dace ayi musu ba."

KU KARANTA: Dalilin da yasa 'yan Najeriya ke korafi kan karin kudin wutar lantarki - Sanusi II

Kazalika, wani lauya kuma mai kare hakkin 'yan adam a jihar, Collins Chidibere ya ce ba zai yiwu kungiyoyin kare hakokin bil adama su cigaba da yin shiru kan cin zarafin da ake yi a jihar ba.

A bangarensa, direktan sashin kula da mutane na Signatious Hotel, Efga Ederoghene cikin sanarwar da ya fitar ya ce ana wannan zargin ne don bata wa Gbagi suna.

Ya ce Gbagi ba shi da hannu ko masaniya a kan lamarin domin yana can yana shirin yadda za ayi jana'izar 'yar uwarsa da ta rasu.

A martaninsa, yayin zantawa da 'yan jarida a ranar Talata, tsohon ministan ya ce bashi da hannu a lamarin amma ya bada umurnin ayi bincike.

Ya ce ya mika gudanar da harkokin otel din a hannu wasu ne.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Onome Onovwakpoyeya ta ce ba ta da masaniya cewa an tube wa ma'aikatan kaya.

A wani labarin daban, wani dan sanda a yayin zaben gwamnan jihar Edo na shekarar 2020 ya nemi toshiyar baki daga hannun jami'in sa ido a kan zabe na Premium Times a ranar Asabar.

Dan sandan da aka tura ya yi aiki a Okada Junction da ke kan babban titin Sagamu - Ibadan ya tsayar da dan jaridar ya hana shi wucewa duk da ya nuna masa katin shaidar aikinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164