Katin gayyatar ɗaurin auren Bashir El-Rufai da Nwakaego ya fito

Katin gayyatar ɗaurin auren Bashir El-Rufai da Nwakaego ya fito

- Za a daura auren Bashir El Rufai da Halima Nwakaego Kazaure a ranar Asabar 21 ga watan Nuwamba

- Hakan na kunshe ne cikin katin gayyatar daurin auren da Bashir El Rufai, dan gwamnan Jihar Kaduna ya wallafa a shafinsa na Twitter

- An bukaci dukkan wadanda ba za su samu hallartar daurin auren ba su yi wa ma'auratan addu'ar fatan alheri da zaman lafiya

Daga karshe dai katin auren dan gwamnan Jihar Kaduna Bashir El-Rufai da Halima Nwakaego Kazaure ya fito.

Za a daura auren ne a ranar Asabar 21 ga watan Nuwamban shekarar 2020 misalin karfe 11 na safe.

Ana sa ran za a daura auren ne a gida mai lamba 11B 2nd Street, Ministers Quaters Mabushi a babban birnin tarayya Abuja kamar yadda ya ke rubuce a katin gayyatar.

Katin gayyatar ɗaurin auren Bashir El-Rufai da Nwakaego ya fito
Katin gayyatar ɗaurin auren Bashir El-Rufai da Nwakaego ya fito. Hoto: @BelloElRufai
Asali: Twitter

Amaryar lauya ce kuma diya ga Sanata Ibarhim Kazaure OFR.

Ga wadanda ba za su samu ikon hallartar daurin auren ba an bukaci su taimaka da addu'ar fatan yin bikin lafiya da zaman lafiya ga ma'auratan.

Ga dai katin gayyatan auren nan a kasa kamar yadda Bashir El Rufai ya wallafa a shafinsa na Twitter.

KU KARANTA: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

Katin gayyatar ɗaurin auren Bashir El-Rufai da Nwakaego ya fito
Katin gayyatar ɗaurin auren Bashir El-Rufai da Nwakaego ya fito. Hoto: @BelloElRufai
Asali: Twitter

Kafin fitowar katin auren, Bashir El-Rufai ya wallafa hotunan kafin daurin auren tare da amaryarsa Halima Nwakaego wadda ya janyo cece-kuce da dandalin sada zumunta.

Mutane da dama sun nuna rashin dacewar irin tufafin da Halima ta saka da kuma irin yadda angon da amaryar ke runguma juna ko wani abu mai kama da haka da a cewar mutanen ya sabawa addinin musulunci da dabi'ar bahaushe.

Amma Bashir El-Rufai ya mayar musu da martani inda ya ce ba su san abinda suke yi ba kuma bai nemi shawarsu ba har ma daga bisani cewa ya yi ya gwammace a datse masa wuya a maimakon ya nemi afuwarsu.

DUBA WANNAN: Wike ya ce wani gwamnan PDP daya zai sake fita daga jam'iyyar

Ya kuma wallafa wasu rubutu a shafinsa na Twitter da ke yi wa masu neman yi masa katsalandan habaici kan cewa su fuskanci abinda ke gabansu su kyalle mutane suyi rayuwarsu.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel