Buhari ya mika sakon gaisuwa ga tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayinda ya cika shekaru 63
- Shugaba Muhammadu Buhari ya aika sakon gaisuwa ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yayinda ya cika shekaru 63 a duniya
- Buhari ya jinjinawa Jonathan a kan irin gudunmawar da ya ba kasar da kuma kokarin da yake na kawo zaman lafiya a kasar Mali
- Ranar Juma'a, 20 ga watan Nuwamba ne zai yi daidai da zagayowar ranar haihuwar tsohon shugaban kasar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
A ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamba ne tsohon Shugaban kasar zai cika shekaru 63 a duniya.
A wata sanarwa da kakakin Shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa Buhari ya jinjinawa Jonathan a kan aikinsa wanda ya kawo martaba da alkhairai ga kasar.
KU KARANTA KUMA: Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ziyarci sabon sarkin Zazzau, Nuhu Bamalli
Shugaban kasar ya kuma nuna godiya a kan tsani na musamman da tsohon Shugaban kasar ya hau a siyasar Najeriya, da kuma jajircewarsa a kan aikin da yake yi a baya bayan nan a matsayin wakilin kungiyar ECOWAS domin kawo zaman lafiya a kasar Mali.
Yayinda tsohon Shugaban kasar ya cika shekaru 63, shugaba Buhari ya yi addu’an Allah ya ba Jonathan tsawon rai, lafiya mai nagarta da Karin sani domin ci gaba da yi wa al’umma hidima.
KU KARANTA KUMA: An kashe wani tsohon manajan kamfanin NNPC
A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya yabawa David Umahi, gwamnan Ebonyi, saboda chanja sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya nuna yadda Buhari ya yabi Umahi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng