Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ziyarci sabon sarkin Zazzau, Nuhu Bamalli

Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ziyarci sabon sarkin Zazzau, Nuhu Bamalli

- Mallam Muhammadu Sanusi II ya kai ziyarar ban girma masarautar Zazzau

- Sanusi ya ziyarci Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli domin taya shi murnar nadinsa da mallaka masa sandar girma

- Ya kuma ziyarci kamarin tsohon sarki, Alhaji Shehu Idris sannan ya je ya yi ta'aziyya ga iyalan tsohon gwamnan Kaduna, Balarabe Musa

Tsohon sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi II a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba, ya ziyarci sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli.

Solacebase ta ruwaito cewa Sanusi ya kai wa Bamalli ziyarar taya murna ne a kan nadinsa da kuma gabatar masa da sandar girma da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai yayi.

Da farko dai Sanusi ya isa garin Kaduna a cikin jirgi mai tashi da saukar ungulu, da misalin karfe 8:15 na safe sannan ya garzaya Zariya da misalin karfe 10:45 na safe.

Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ziyarci sabon sarkin Zazzau, Nuhu Bamalli
Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ziyarci sabon sarkin Zazzau, Nuhu Bamalli Hoto: Solacebase
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Hotunan Bashir El-Rufai da amaryarsa ya janyo cece-kuce

Ya taya sabon Sarki Nuhu Bamalli murna sannan ya je kabarin tsohon sarkin Zazzau, marigayi Alhaji Shehu Idris don yi masa addu’a.

Tsohon sarkin na Kano ya kuma gana da iyalan sabon sarkin, hakimai da masu rike da mukamin sarauta. Bayan nan sai ya koma Kaduna tare da sarkin Zazzau.

Hakazalika, Malam Sanusi ya je ya yi ta’aziyya ga iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Marigayi Balarabe Musa wanda ya rasu a ranar Laraba da ta gabata.

KU KARANTA KUMA: Hotunan aure: Bidiyon yadda amarya ta hana angonta ya sumbace ta saboda ta yi kwalliya

A wani labari na daban, a daren Talata wasu bata-gari da ba a san ko su wanene ba, suka fasa ofishin babban Alkalin kotun Dogarawa, Mai Shari'a Kabir Dabo, wanda yake shari'a tsakanin sabon sarki, Ahmed Bamalli da Iyan Zazzau, Bashir Aminu.

Sai da bata-garin suka fasa kotun, tukunna suka samu damar shiga har ofishin babban alkalin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel