An kashe wani tsohon manajan kamfanin NNPC

An kashe wani tsohon manajan kamfanin NNPC

- Yan bindiga sun kashe wani tsohon manajan kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), Cif Gregory Duruiheakor

- Makasan sun harbi Duruiheakor a kirji a gidansa da ke yankin New Owerri, jihar Imo

- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar al'amarin

Wasu da ake zargin makasa ne sun kashe tsohon manajan kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), Cif Gregory Duruiheakor.

An harbe Duruiheakor a gidansa da ke yankin New Owerri na Owerri, babbar birnin jihar Imo.

Marigayin ya fito ne daga yankin Atta da ke karamar hukumar Njaba.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa yan daba sun kai farmaki gidan nasa a daren ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA KUMA: Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ziyarci sabon sarkin Zazzau, Nuhu Bamalli

An kashe wani tsohon manajan kamfanin NNPC
An kashe wani tsohon manajan kamfanin NNPC Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Daya daga cikin yan uwansa ya tabbatar da lamarin. Ya ce: “Har yanzu muna cikin alhini game da mutuwar Cif Duruiheakor. Bayanai da muka samu ya nuna cewa an harbe shi ne a kirjinsa sannan ya mutu a nan take. Abun bakin ciki ne kuma mun kira yan sanda domin su gudanar da bincike a kan al’amarin."

Kakakin yan sandan jihar, Orlando Ikeokwu ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce Duruiheakor ya mutu kafin ya kai asibiti.

KU KARANTA KUMA: Hotunan aure: Bidiyon yadda amarya ta hana angonta ya sumbace ta saboda ta yi kwalliya

A gefe guda, jami'an sintirin jihar Kaduna (KADVIS) sun gamu da ajalinsu yayin arangama da yan bindiga a karamar hukumar Chikun, da yammacin Talata, a cewar wani jami'i.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka ranar Laraba kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ya kuma ce daga baya sojoji sun yi nasarar kashe yan tawayen da suka kaiwa jami'an hari, a kauyen Dande a babban garin Bukuru.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel