Zargin da ake yi mana ba gaskiya ba ne inji Gwamnatin jihar Akwa-Ibom
- Wata kungiya ta zargi Gwamnan Akwa Ibom da facakar biliyoyin kudi
- Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta musanya wannan zargi, ta yi karin haske
- Kwamishinan kasafi ya fitar da wasu alkaluma da ya ce su ne na gaskiya
ICRI ta zargi gwamnatin jihar Akwa Ibom a karkashin @MrUdomEmmanuel da kashe N5.04bn wajen kula da jirgin saman jihar.
Kudin da aka kashe ya zarce abin da majalisar dokokin jihar ta ware na N2.5bn domin wannan aiki.
Bayan haka ana zagin ofishin sakataren gwamnati da na shi kansa mai girma gwamna da kashe kudin da ba su cikin kasafin jihar.
KU KARANTA: Abin da ya sa haduwarmu da Gwamnonin Kudu ba ta yiwu ba - Buhari
Ana zargin gwamnatin Emmanuel da batar da abin da ya zarce biliyan 10 a kan motoci, jiragen sama, kudin mai da kuma tarbar baki.
Gwamnatin Akwa Ibom ta ce akwai kura-kurai a tattare da alkaluman da kungiyar ta samu, don haka ta fayyace yadda lamarin ya ke.
Kwamishinan cigaban tattalin arzikin Akwa Ibom, Akan Okon ya zauna da manema labarai domin ya yi karin haske a jiya ranar Laraba.
Mista Akan Okon ya ce bayanan da aka dogara da su daga ofishin mai binciken kudi na jihar, cike suke da kura-kuran da tuni aka yi gyara.
KU KARANTA: Wani Gwamnan PDP zai koma APC
Kwamishinan ya ce tun a watan Satumba aka fitar da jawabi, inda aka janye rahoton da mai binciken kashe kudi na jihar ya gabatar.
Daga cikin kuren shi ne an kashe N2.7b wajen sayen mai, ainihin abin da aka kashe shi ne N1.3b, an kuma yi kari a kan kudin sayen motoci.
Kwamishinan ya ce miliyan 800 aka kashe wajen sauke baki, ba N1.18b da aka rahoto a baya ba.
‘Yan Majalisa da Sanatocin PDP na Ebonyi sun ce ba za su bi gwamnan zuwa jam'iyyar APC ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng