Babu ruwanmu da Umahi, mu na nan a Jam’iyyar PDP inji ‘Yan Majalisan Ebonyi
- ‘Yan Majalisar Tarayya najihar Ebonyi sun ce ba za su shiga tafiyar APC ba
- Duk da Gwamna David Umahi ya bar PDP, ‘Yan majalisar za su yi zamansu
- Babu wani Dan majalisar wakilai ko Sanatan PDP a Ebonyi da zai canza sheka
Punch ta fitar da rahoro ‘yan majalisar tarayya daga jihar Ebonyi sun yi magana game da sauya-shekar da gwamna David Umahi ya yi daga jam’iyyar PDP.
‘Yan majalisar wakilan tarayya da na majalisar dattawa da su ka fito daga Ebonyi, sun ce babu abin da ya hada su da jam’iyyar APC da gwamnan ya koma.
Shugaban ‘yan majalisar Ebonyi, Sanata Sam Egwu, ya bayyana haka a madadin abokan aikinsa.
KU KARANTA: Shugabannin NWC sun korri masu rike da Jam’iyya a Ebonyi
Jaridar ta ce Sam Egwu ya karanta takarda gaban ‘yan jarida inda ya tabbatar da matsayar da duk ‘yan majalisar tarayya na Ebonyi su ke kai game da lamarin.
Tsohon gwamnan ya yi wannan jawabi ne a gaban ‘yan jarida ranar Talata a birnin tarayya Abuja.
Egwu ya ke cewa babu wani ‘dan majalisa da zai tattara ya bi Dave Umahi zuwa sabuwar jam’iyyarsa ta APC, ya ce dukkansu suna nan a jam’iyyar PDP.
‘Yan majalisar sun nuna rashin amincewa da dalilan da gwamnan ya bada a matsayin abin da ya sa ya yi watsi da jam’iyyar da ta taimaka masa ya lashe zabe.
KU KARANTA: Laifi 1 da na yi wa PDP - Umahi
Kamar yadda wasu manyan PDP su ke zargi, ‘yan majalisar jihar Kudu maso kudun sun zargi gwamna Umahi da cewa son-kai ya tunzura shi ya koma APC.
Har zuwa yanzu ba a san matsayar ‘yan majalisar dokokin jihar Ebonyi ba, watakila a samu wasu da za su fice daga PDP mai rinjaye, su bi gwamnan zuwa APC.
Wike ya ce kwadayin mulki ya sa Umahi ya sauya-sheka ba rashin adalcin da ya ke fada ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng