Bidiyon yadda yan achaba suka fatattaki jami’an yan sanda a Lagas

Bidiyon yadda yan achaba suka fatattaki jami’an yan sanda a Lagas

- Wasu yan achaba sun fatattaki jami'an yan sanda da gudu a yankin Ikeja da ke jihar Lagas

- Lamarin ya afku ne a yau Laraba, 18 ga watan Nuwamba, inda aka gano yan sandan suna gudu ba kama hannun yaro

- Jami'an tsaron sun je yankin ne domin kama yan achaban da ke karya dokar ka'idar tuki

Jami’an yan sanda sun ci na kare a yau Laraba, 18 ga watan Nuwamba, bayan yan achaba sun fatattake su a hanyar babban titin Lagos-Abeokuta da ke yankin Ikeja, jihar Lagas.

A wani bidiyo da ya shahara, an gano wasu yan achaba suna bin jami’an tsaro da gudu, yayinda su kuma suka shige motarsu na aiki sannan suka bar wajen a guje.

An tattaro cewa jami’an tsaron sun je yankin ne domin kama baburan da suke take dokar tuki a jihar.

Bidiyon yadda yan achaba suka fatattaki jami’an yan sanda a Lagas
Bidiyon yadda yan achaba suka fatattaki jami’an yan sanda a Lagas Hoto: Lindaikejiblog
Asali: UGC

Lamarin na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan wasu masu achaba sun kara da rundunar tsaro a yankin Festac da ke jihar.

KU KARANTA KUMA: Allah ya azurta ma’auratan da suka yi shekaru 6 ba haihuwa da ‘yan uku shekaru 3 bayan sun karbi rikon wata yarinya

Ga bidiyon karawar kamar yadda shafin Lindaikejiblog ya wallafa:

KU KARANTA KUMA: Ganduje: Hukumar yaƙi da rashawa ta Kano ta fi kowacce tasiri a Nigeria

A wani labari, rundunar yan sanda a jihar Lagas a ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, ta bayyana cewa ta kama mutane 720 mabuya daban-daban a jihar duk a cikin kokarin da ake na kakkabe laifuka.

Olumuyiwa Adejobi, kakakin yan sandan jihar, a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa rundunar ta kai samamen ne a ranar Lahadi sannan ta kama masu laifin a yankuna 14.

An kuma samo makamai, layoyi, da miyagun kwayoyi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel