PDP: Uwar-Jam’iyya ta rusa shugabannin Ebonyi bayan tashin Dave Umahi

PDP: Uwar-Jam’iyya ta rusa shugabannin Ebonyi bayan tashin Dave Umahi

- NWC ta ruguza duk shugabannin Jam’iyyar PDP da ke jihar Ebonyi

- Shugabannin rikon kwarya na PDP a Kudu sun rasa mukamansu

- Jam’iyyar adawar ta yi wannan ne bayan Dave Umahi ya tafi APC

Sauyin-shekar gwamna David Umahi ta fara tasiri a Ebonyi, inda yanzu har an fatattaki daukacin shugabannin jam’iyyar hamayyar da ke jihar.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa uwar-jam’iyyar PDP ta yi fatali da majalisar shugabannin jam’iyyar da ke aiki a kananan matakai na jihar.

Shugabannin PDP na mazabu, kananan hukumomi da kuma majalisar jiha sun rasa mukamansu.

KU KARANTA: Jigon APC ya ajiye mukaminsa saboda Umahi

Majalisar NWC da ke da alhakin gudanar da sha’anin jam’iyya ta bayyana haka a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba, ta bakin Kola Ologbondiyan.

Kola Ologbondiyan wanda shi ne sakataren yada labarai na jam’iyyar hamayyar, ya bada wannan sanarwa.

Mista Ologbondiyan ya ce NWC ta dauki wannan matsaya ne bayan wani zama na musamman da shugabannin jam’iyyar PDP su ka yi a ranar Talata.

Bayan haka, Ologbondiyan ya bayyana cewa NWC ta ruguza majalisar shugabannin rikon-kwarya na jam’iyyar da ke rike da shiyyar Kudu maso gabas.

KU KARANTA: Gwamnonin Jihohi masu-ci da su ka tsere daga Jam’iyyarsu

PDP: Uwar-Jam’iyya ta rusa shugabannin Ebonyi bayan tashin Dave Umahi
Dave Umahi Hoto: @EbonyiGov
Asali: Twitter

Kamar yadda kakakin jam’iyyar hamayyar ya fada, dokar kasa da kundin PDP sun ba majalisar NWC ikon sauke duk wasu shugabanni idan ta kama.

Kawo yanzu, uwar-jam’iyyar ba ta bayyana wadanda za su rike guraben na rikon kwarya a jihar Ebonyi da yankin kasar kafin a gudanar da zabe ba.

A makon nan mun ji cewa tsohon gwamna jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, yana da burin zama shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa na 2023.

Okorocha ya sanar da hakan ne bayan wasu taron magoya bayansa sun kai masa ziyara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng