Rabon kwado: Gwamna Inuwa Yahaya ya ba wanda ya yi wa Buhari tattaki kyautar mota da N2m

Rabon kwado: Gwamna Inuwa Yahaya ya ba wanda ya yi wa Buhari tattaki kyautar mota da N2m

- Gwamna Muhammadu Yahaya na jihar Gombe, ya yi wa mutumin da ya yi tattaki saboda Buhari a 2015 kyautar mota

- A makon da ya gabata ne mutumin mai suna Dahiru Buba ya nemi a kawo masa doki shekaru biyar bayan ya yi tattaki daga Abuja zuwa Gombe

- Gwamnan ya ce ya yi umurnin daukar Buba a kai asibiti domin bashi cikakken kulawa

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya bai wa mutumin da ya yi tattaki daga Gombe zuwa Abuja domin murnar nasarar zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015 kyautar mota.

Har ila yau, gwamnan ya bai wa mutumin mai suna Dahiru Buba Dukku zunzurutun kudi har naira miliyan biyu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai ba wa gwamnan shawara a kan kafofin watsa labarai, Ismal Uba Misili, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Rabon kwado: Gwamna Inuwa Yahaya ya ba wanda ya yi wa Buhari tattaki kyautar mota da N2m
Rabon kwado: Gwamna Inuwa Yahaya ya ba wanda ya yi wa Buhari tattaki kyautar mota da N2m Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kashe Hakimin Gidan Zaki tare da mutane 3 a Kaduna

A yanzu haka, Buba mai shekaru 50 na fama da matsalar ciwon kafa. An kuma mika mashi kyautar ne a babbar birnin tarayya Abuja, a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba.

A cewar sanarwar, gwamnan ya ba shi kyautar ne saboda tsananin kaunar da yake yi wa jam'iyyar APC mai mulki a kasar

Rabon kwado: Gwamna Inuwa Yahaya ya ba wanda ya yi wa Buhari tattaki kyautar mota da N2m
Rabon kwado: Gwamna Inuwa Yahaya ya ba wanda ya yi wa Buhari tattaki kyautar mota da N2m Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

Rabon kwado: Gwamna Inuwa Yahaya ya ba wanda ya yi wa Buhari tattaki kyautar mota da N2m
Rabon kwado: Gwamna Inuwa Yahaya ya ba wanda ya yi wa Buhari tattaki kyautar mota da N2m Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

A baya mun kawo maku cewa Dahiru Buba, wanda yayi tattaki domin murnar nasarar da shugaba Muhammadu Buhari yayi a zaben 2015 yana fama da ciwon kafa.

Buba na neman taimakon jama'a saboda kafar ta tasa shi gaba. Dahiru Buba, wanda dan asalin Karamar Hukumar Dukku ne a Jihar Gombe, yana daya daga cikin mutanen da suka yiwa shugaba Buhari tattaki daga jihohinsu zuwa birnin tarayya Abuja.

Wanda yafi shahara cikinsu shine Hamisu Treaker.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da shugabannin tsaro a fadar Shugaban kasa

Yanzu Dahiru Buba na fama da ciwon kafa mai tsanani, kuma yana mika kokon baransa zuwa ga uwar jam’iyyar APC ta taimaka masa da abin da zai yi amfani da shi wurin jinyar kafar tasa.

A cewar Aminiya, Dahiru ya kwashe kwanaki 15 a hanya yayinda yayi tattakinsa zuwa Abuja.

Dahiru ya bayyana cewa tun lokacin da yayi wannan tattaki bai sake jin dadin kafarsa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel