Da ɗuminsa: Atiku Abubakar ya miƙa ƙoƙon bara ga mambobin PDP na shiyyar Kudu kan zaben 2023

Da ɗuminsa: Atiku Abubakar ya miƙa ƙoƙon bara ga mambobin PDP na shiyyar Kudu kan zaben 2023

- An bukaci mutanen kudu maso gabas da sauran yankuna da kada su bar PDP

- Atiku Abubakar wanda ya bukaci yan Najeriya da su yi imani da babbar jam’iyyar adawar kasar ne ya yi wannan rokon

- Wasu mutane sun yi barazanar barin jam’iyyar zuwa APC domin cimma shugabancin Igbo a 2023

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin Shugaban kasa, ya bukaci dukkanin yankunan kasar, da kada su bar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) gabannin zaben 2023.

PM News ta ruwaito cewa sakon tsohon mataimakin Shugaban kasar na magana ne a kan mambobin jam’iyyar a kudu maso gabas.

Legit.ng ta tattaro cewa akwai rahotanni da ke nuna cewa mambobin jam’iyyar a kudu maso gabas na shirin barin PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki kan matakin jam’iyyar na kin bai wa yankin tikitin takarar Shugaban kasa na 2023.

KU KARANTA KUMA: Rabon kwado: Gwamna Inuwa Yahaya ya ba wanda ya yi wa Buhari tattaki kyautar mota da N2m

Da ɗuminsa: Atiku Abubakar ya miƙa ƙoƙon bara ga mambobin PDP na shiyyar Kudu kan zaben 2023
Da ɗuminsa: Atiku Abubakar ya miƙa ƙoƙon bara ga mambobin PDP na shiyyar Kudu kan zaben 2023 Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Shugaban PDP da sauran jiga-jigan jam’iyyar sun sha fadin cewa ba za su mika tikitin takarar Shugaban kasa na 2023 ga yankin kudancin kasar ba.

Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya bayyana cewa zai sauya sheka zuwa APC inda yake shirin cimma kudirinsa na shugabantar kasar a 2023.

Akwai kuma rade-radin cewa sauran jiga-jigan PDP a kudu maso gabas na iya binsa a kwanaki masu zuwa a kokarinsu na tabbatar da shugabancin Igbo a 2023.

Atiku, dan arewa daga jihar Adamawa, wanda ake ganin yana kokarin ganin ya mallaki tikitin Shugaban kasa na PDP a 2023 a wani wallafan sassafe da ya yi a shafin Twitter a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, ya yi martani ga rade-radin.

Ya roki kudu maso gabas da sauran yankuna a kan kada su bar jam’iyyar wanda a cewarsa, ita ce aminiyar Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kashe Hakimin Gidan Zaki tare da mutane 3 a Kaduna

Ya ce: “Jam’iyyar Peoples Democratic Party ce aminiyar da Najeriya za ta iya samu. Dukkanin yankunan kasar sun cancanci jam’iyyar siyasa da ta yi imani da Najeriya ba wai jam’iyyar da take sabanin haka ba.

“Jam’iyyar @OfficialPDPNig tana da tarin alkhairai da za ta gabatarwa da dukkanin yankunan Najeriya, kuma ina bukatan yan Najeriya a dukkanin yankuna da su yi imani da jam’iyyar da za ta yi adalci ga kowa."

A gefe guda, jaridar Punch ta ce jam’iyyar APC ta na hobbasa na ganin ta jawo hankalin wasu gwamnonin hamayya a yankin Kudu maso gabashin Najeriya.

Jam’iyyar APC mai mulki ta na zawarcin kusoshin adawar ne bayan maganar sauya-shekar gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi daga PDP.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags:
APC