Trump ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen Amurka
- Har yanzu cece-kuce da hargowa ta ki ta kare a kan zaben kujerar shugaban kasar Amurka da aka gudanar a farkon watan nan
- Dan takarar jam'iyyar Democrta, Sanata John Kerry, ne a gaba a yawan dukkkan kuri'un da ke bawa dan takara nasara
- Sai dai, shugaba Trump, mai takara a jam'iyyar Republican ya ce sam ba zai taba karbar wani sakamako da bai bashi nasara ba
Shugaba Donald Trump ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe halastaccen zaɓen Amurka na bana, 2020, duk da kayen da ya sha a hannun abokin karawarsa, Joe Biden, na jam'iyyar Democrat bisa alƙaluman ƙuri'u da aka tattaro.
Biden shine akan gaba a dukkanin zaɓukan fili da ɓoye tuni aka bayyana shi a matsayin zakaran zaɓen kuma shugaban ƙasa Amurka na gaba.
KARANTA: Janar Abubakar Sa'ad ya shigar da karar Buratai, ministan tsaro, da ilahirin rundunar soji
Sai dai,Trump yana ta maganganu game da zaɓen inda ya wallafa a shafinsa na Tiwita a jiya,yana mai cewar: "Ni na lashe zaɓe," a cewar Trump yayin da yake sake tura saƙon da ya rubuta;
"Me yasa labaran ƙanzon kurege suke cigaba da zagayawa akan Joe Biden zai hau kujerar mulkin ƙasa,ba tare da sun bar ɓangaren mu sun nuna matsayar su ba,bayan yanzu muka fara shirin nuna yadda aka karya da kuma watsi da dokoki da tsaren ƙasar mu lokacin gudanar da zaɓen shekarar 2020.
KARANTA: 'Yan bindiga sun sace ASP 12 daga tawagar 'yan sanda a tsakanin Katsina-Zamfara
"An kai farmaki a kan tsarin zaɓen mu, tabbas idan akayi la'akari da yawan adadin masu sa ido akan zaɓen da aka fitar daga ɗakin ƙirga ƙuri'u a jihohi da dama, akwai miliyoyin ƙuri'u da Democrat suka canja don ƙarawa jam'iyyarsu yawan ƙuri'u, sannan kuma sun yi zaɓe bayan lokacin zaɓe ya wuce, ga kuma son rai irin wanda suka nuna na hana jama'a zaɓen wata jam'iyyar da ba tasu ba a Texas da sauran wurare masu yawa.
"Saboda hakan ba abune mai kyau ba, waɗanda keda alhakin kare dokokin ƙasar nan,nauyi ya rataya a wuyansu na ganin basu bar sakamakon bogi da akayi amfani dashi a zaɓen 2020 na wasiƙa(Mail in Election) tasiri ba. Duniya tana kallo," a cewar Trump.
Legit.ng ta sha kawo rahotanni a kan yadda tun kafin a gudanar da zabe Trump ya ki amsa tambayar ko zai mika mulki idan ya fadi zaben kujerar shugaban kasa a Amurka.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng