Janar Abubakar Sa'ad ya shigar da karar Buratai, ministan tsaro, da ilahirin rundunar soji

Janar Abubakar Sa'ad ya shigar da karar Buratai, ministan tsaro, da ilahirin rundunar soji

- Birgediya Janar Abubakar Sa'ad (mai ritaya) ya shigar da karar ilahirin rundunar soji a gaban kotun ma'aikata

- Tsohon sojan ya shigar da karar rundunar soji da jagorinta bayan an yi masa ritayar dole daga aiki

- Mohammed Adelogun, lauyan mai kara, ya ce kotu ta saka lokacin sauraron korafin da suka shigar, sai dai akwai tarnaki

A ranar Talata ne birgediya janar (mai ritaya), Abubakar Sa'ad, ya shigar da karar ilahirin rundunar soji a gaban kotun ma'aikata (NIC) domin kalubalantar yi masa ritayar dole.

Sauran wadanda mai korafin ya ambata a cikin takardar shigar da kara sun hada da, babban hafsan rundar soji; Laftanal Janar Tukur Buratai, shugaban rundunar tsaro; Janar Abayomi Olanisekin, da kuma ministan tsaro; Bashir Salihi Magashi, da kuma majalisar koli da rundunar soji.

KARANTA: 'Yan bindiga sun sace ASP 12 daga tawagar 'yan sanda a tsakanin Katsina da Zamfara

Lauyan mai kara, Mohammed Adelogun, ya ce kotu ta saka lokacin sauraron korafin da suka shigar.

A cewar lauyan, an fara shigar da karar ne a ranar 7 ga watan Satumba, 2016, amma sai kotu ta yi watsi da karar a ranar 16 ga watan Satumba, 2017, saboda rashin cika wata ka'ida.

Mista Adelogun ya ce kotu ta yi watsi da karar ne bayan wadanda ake kara sun yi korafin cewa mai kara ya sabawa tanadin dokar rundunar soji, kafin ya shigar da kara.

Janar Abubakar Sa'ad ya shigar da karar Buratai, ministan tsaro, da ilahirin rundunar soji
Ministan tsaro; Bashir Magashi, yayin gabatar da kasafin ma'aikatar tsaro a majalisa
Asali: Facebook

Lauyan ya kara da cewa mai kara ya kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara a cikin shekarar 2018, inda daga bisani kotun daukaka kara ta jingine hukuncin kotun farko.

KARANTA: Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Katsina, sun kashe na kashewa, sun kwaci makamai da dukiya

Kotun daukaka kara ta bukaci a mayar da karar zuwa kotun NIC domin a saurari korafin birgediya janar Sa'ad, a cewar lauya Adelogun.

Kazalika, Lauyan ya bayyana cewa wadanda ake kara sun sake dakirewa, suna masu gardamar cewar tuni an gama da maganar, babu wani sauran zance, hasalima, sun ce; kotun ba ta da ikon sauraron korafin.

Ya bayyana cewa ya yi raddi ga martanin wadanda ake kara, sannan ya nemi izinin sauya wani bangare na korafinsu tare da bawa kotu hakuri a kan shigar da kara a kurarren lokaci.

Kwamanda a rundunar soji ya yanke jiki ya fadi matacce yayin da ya ke tsaka da gabatar jawabi ga sojoji a wurin bayar da horo a kan yaki da Boko Haram a jihar Borno.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel