Ciwon kafa ta tasa mutumin da yayi tattaki don nasarar Buhari gaba

Ciwon kafa ta tasa mutumin da yayi tattaki don nasarar Buhari gaba

- Masoyin Buhari kuma dan jam'iyyar APC yana kira ga uwar jami'yya ta kawo masa dauki

- Yana fama da ciwon kafa bayan tattakin da yayi daga jiharsa zuwa Abuja don murnar nasarar Buhari

- Shugaba Buhari ya doke tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, a zaben 2015

Wani mutumi mai suna Dahiru Buba, wanda yayi tattaki domin murnar nasarar da shugaba Muhammadu Buhari yayi a zaben 2015 yana fama da ciwon kafa.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Buba na neman taimakon jama'a saboda kafar ta tasa shi gaba.

Dahiru Buba, wanda dan asalin Karamar Hukumar Dukku ne a Jihar Gombe, yana daya daga cikin mutanen da suka yiwa shugaba Buhari tattaki daga jihohinsu zuwa birnin tarayya Abuja.

Wanda yafi shahara cikinsu shine Hamisu Treaker.

Yanzu Dahiru Buba na fama da ciwon kafa mai tsanani, kuma yana mika kokon baransa zuwa ga uwar jam’iyyar APC ta taimaka masa da abin da zai yi amfani da shi wurin jinyar kafar tasa.

A cewar Aminiya, Dahiru ya kwashe kwanaki 15 a hanya yayinda yayi tattakinsa zuwa Abuja.

Dahiru ya bayyana cewa tun lokacin da yayi wannan tattaki bai sake jin dadin kafarsa ba.

“Tun daga lokacin dana gudanar da tattakin kafata ta hana ni sakat, hakika zan ji dadi idan jam’iyyar ta taimaka min na warke, " yace.

KU KARANTA: Inda Najeriya da kasashen Afrika za su tsinci kansu karkashin mulkin Biden

Ciwon kafa ta tasa mutumin da yayi tattaki don nasarar Buhari gaba
Ciwon kafa ta tasa mutumin da yayi tattaki don nasarar Buhari gaba Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA NAN: Buhari ya aike wa matasa muhimmin sako ta hannun Gambari da sarakuna

Mun kawo muku cewa shugaba Muhammadu Buhari ya gana da wakilan sarakunan gargajiyan sassan Najeriya shida, karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar.

Ganawar, da akayi a fadar shugaban kasa, Villa, Abuja ya samu hallaran Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi; Sarkin Kano, Etsu Nupe, Sarakunan yankin Igbo, dss, cewar Vanguard.

Shi ma Amanyanabo na kasar Twon-Brass, Mai martaba Alfred Diete-Spiff da wasu Sarakunan yankin Neja-Delta duk sun samu damar ganin shugaban kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel