Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da shugabannin tsaro a fadar Shugaban kasa
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ganawa da shugabannin tsaro na kasa
- Mataimakin shugaban kasa, manyan jami'an gwamnati da wasu daga cikin ministoci duk sun hallara
- Sai dai babban mai ba shugaban kasa shawara kan tsaron kasa, Babagana Monguno bai isa dakin taron ba a yanzu haka
A yanzu haka, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar tsaro ta kasa, a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.
Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, Ibrahim Gambari.
Sai Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami da ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magaji (mai ritaya).
Sauran da suka hallara sune ministan cikin harkokin cikin, Rauf Aregbesola; ministan harkokin waje, Geoffery Onyeama, da kuma ministan harkokin yan sandan, Muhammad Dingyadi.
KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kashe Hakimin Gidan Zaki tare da mutane 3 a Kaduna
A daidai lokacin kawo wannan rahoton, babban mai ba kasa shawara a kan tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) wanda ya shirya taron bai hallara ba tukuna.
Shugabannin tsaro da suka hallara sune Shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Gabriel Olonisakin; Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai.
Sai kuma Shugaban sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe-Ibas; da Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshall Sadique Abubakar.
Sufeto Janar na yan sanda, IGP Mohammed Adamu; daraktan hukumar liken asiri na kasa; Ahmed Rafa’i Abubakar; da Darakta Janar na rundunar tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Magaji Bichi ma sun hallara.
Ga hotunan ganawar wanda fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta na Twitter:
KU KARANTA KUMA: Covid-19: Yadda muka ciyar da iyalai 127,588 lokacin kulle - Minista Sadiya
A wani labari na daban, mun ji a baya cewa Shugaban majalisar wakilai ya yi ganawar sirri tare da shugabannin hukumomin tsaro a kasar.
Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Wase ne ya jagoranci ganawar wanda aka fara da misalin karfe 2:15 na yau Litinin, 16 ga watan Nuwamba, jaridar Punch ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng