Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kashe Hakimin Gidan Zaki tare da mutane 3 a Kaduna

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kashe Hakimin Gidan Zaki tare da mutane 3 a Kaduna

- 'Yan bindiga sun kashe Hakimin Gidan Zaki da dansa a wani sabon hari da suka kai karamar hukumar Zangon Kataf

- Lamarin ya afku ne a safiyar yau Talata, 17 ga watan Nuwamba

- Hakan na zuwa ne bayan yan bindiga sun kashe mutane 12 a wasu hare-hare da suka kai kauyukan jihar

Yan bindiga sun kashe Haruna Kuye Hakimin Gidan Zaki, a karamar hukumar Zangon Kataf da ke jihar Kaduna da dansa, Destiny Kuye a safiyar yau Talata, 17 ga watan Nuwamba.

Sun kuma tafi da matarsa da yarsa dauke da raunin sara da harbin bindiga.

Jaridar The Nation ta kuma ruwaito cewa an kashe wasu mutane biyu sannan aka yi garkuwa da wasu a wani harin da aka kai kauyukan Fatika, Kaya da Yakawada na karamar hukumar Giwa.

Sabbin hare-haren na zuwa ne yan sa’o’i kadan bayan tabbatar da kisan mutane 11 da yan bindiga suka yi a karamar hukumar Igabi.

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kashe Hakimin Gidan Zaki tare da mutane 3 a Kaduna
Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kashe Hakimin Gidan Zaki tare da mutane 3 a Kaduna Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

Gwamna Nasir El-Rufai wanda ya nuna damuwa kan lamarin, ya umurci kwamishinan yan sanda da daraktan hukumar tsaro ta DSS da su hadu da rundunar soji.

Ya kuma nemi su tsamo makasan hakimin da sauran mutanen da aka kashe a hare-haren.

KU KARANTA KUMA: Ba fa a mulkin soja muke ba; Buba Galadima ya kwankwashi Buhari a kan taba jagororin ENDSARS

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar da sabin hare-haren a cikin wata sanarwa, ya kuma bayyana sunayen mutanen da aka kashe a ranar Litinin.

Ya bayyana sunayensu a matsayin "Amadu Mallam, Idi Gefefe, Isah Goma, Awwalu Goma, Babangida Iliyasu, Lado Iliyasu, Ya’u Jumare, Hamza Umaru, Shehu Jibril, Tukur Albasu and Musa Adamu Muruzuwa."

Wadanda suka jikkata kuma sune Muazu Albasu, Samaila Chairman, Junaidu Husaini da wata mata da ba a gano sunanta ba tukuna.

A cewarsa: “Rundunar soji karkashin Operation Safe Haven sun sanar da gwamnatin jihar Kaduna game da kisan Hakimin Gidan Zaki, Mista Haruna Kuye da dansa, Destiny Kuye a safiyar yau Talata, 17 ga watan Nuwamba. An kashe su ne a gidansu da ke Gidan Zaki, karamar hukumar Zangon Kataf.

“Sojin sun bayyana cewa matar Hakimin ta ji raunin sara da adda a hannunta yayinda yarsa ke dauke da harbin bindiga a yatsarta.

“Rahoton tsaron ya ci gaba da bayyana cewa wasu mutane biyar dauke da bindigogin AK-47 da adduna ne suka aiwatar da harin, sannan suka yi kokarin kona gidan da wani abun hawa.

“Rundunar sojin ta kara da cewa ta gano harsasai a wajen. Rundunar tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro na gudanar da bincike sannan suna bibiyar makasan.

“Gwamna Nasir El-Rufai ya yi Allah-wadai da mummunan aika-aikan da makiyan zaman lafiya suka aiwatar , ya kuma ce dole a tsamo su domin su fuskanci doka."

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Yadda muka ciyar da iyalai 127,588 lokacin kulle - Minista Sadiya

Ya kara da cewa, Gwamna Nasir El-Rufai, ya tura da sakon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda al'amarin ya shafa, da kuma fatan Allah yayi musu rahama.

A gefe guda, Gwamnan jihar Katsina, Bello Masari, a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, ya koka kan ayyukan yan bindiga a jiharsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng