Ba fa a mulkin soja muke ba; Buba Galadima ya kwankwashi Buhari a kan taba jagororin ENDSARS
- Buba Galadima ya yi Allah-wadai da daskarar da asusun bankunan wasu jagororin zanga zangar EndSARS da gwamnati ta yi
- Galadima ya tunatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa a mulkin damokradiyya ake ba na sojoji ba
- Ya ce sam gwamnati bata da yancin daukar wannan mataki a kan masu zanga zangar
Buba Galadima, tsohon aminin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi watsi da takunkumin da aka sanya wa wasu masu zanga zangar EndSARS.
Babban bankin Najeriya (CBN) ya samu wani umurnin kotu, inda ta umurci wasu bankuna da su daskarar da asusun mutane 19 da wani kamfani da ka alakanta da zanga zangar EndSARS kan zargin daukar nauyin ta’addanci.
Modupe Odele, wata mai kare hakkin dan adam wacce ta taimakawa mutanen da aka kama a yayin zanga zangar, ta ce hukumar kula da shige da fice ta kwace mata fasfot dinta.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai na cikin ganawar sirri da shugabannin tsaro
Da yake magana a lokacin da ya bayyana a shirin Arise TV a ranar Litinin, Galadima ya bukaci Buhari da ya yi umurnin bude asusun bankunan da aka daskarar.
Galadima ya bayyana yunkurin a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulki, sannan ya tunatar da Shugaban kasar cewa Najeriya na mulkin damokradiyya ne ban a sojoji ba.
”Abunda gwamnati ta yi ba daidai bane. Bata da ikon hana yan Najeriya tafiya zuwa wajen kasar ko kuma hana su iko da asusun bankunansu. Daskararwa kan wani dalili? Me suka yi?” Galadima ya tambaya.
KU KARANTA KUMA: Yawancin yan bindigar da ke Katsina daga Zamfara suke shigowa, in ji Gwamna Masari
“Wadannan matasa sun yi zanga zangar lumana ne a kan hukumomin gwamnati. Me yasa bayan kun lallashe su ko bayan jami’an gwamnati sun far masu ko kashe su, sannan kuka dauki wannan mataki na toshe asusun bankunansu? Wannan baya bisa kundin tsarin mulki.
“Ina aika wannan sakon zuwa ga shugaban kasa imma ya sani ko bai sani ba, a nuna masa abunda na fadi. Mutanensa basu da hakkin yin abunda suke yi.
“Dan Allah su janye sannan su bude asusun wadannan matasa sannan su barsu su gudanar da harkokinsu a matsayinsu na yan Najeriya. Ba za ku iya razana su ba. Muna mulkin damokradiyya ne ba na sojoji ba.”
A baya mun ji cewa an maka yan Najeriya hamsin a bangarori daban-daban da suka hada da mawaki David Adeleke, jagorar #BringBackourGirls, Aisha Yesufu da kuma Fasto Sam Adeyemi a gaban kotun majistare da ke Abuja.
An kai su kotu ne a kan rawar ganin da suka taka a zanga zangar EndSARS da aka yi kwanan nan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng