Yawancin yan bindigar da ke Katsina daga Zamfara suke shigowa, in ji Gwamna Masari
- Yan bindiga na ta’asa a Katsina sannan su tsere zuwa Zamfara don buya
- Wannan shine matsayar Gwamna Bello Masari na jihar Katsina
- Masari ya kara da cewa kimanin 99% na miyagun da ke garkuwa da mutane, kisa da sata a jiharsa sun fito ne daga Zamfara
Gwamnan jihar Katsina, Bello Masari, a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, ya koka kan ayyukan yan bindiga a jiharsa.
Masari, wanda ya yi magana da manema labarai a Kafur ya bayyana cewa mafi akasarin wadannan miyagun su kan je su haddasa tashin hankali a Katsina sannan su koma mabuyarsu a Zamfara, jaridar The Nation ta ruwaito.
Gwamnan ya yi korafin cewa yan bindigan na yin duk abunda za su iya don wargaza kokarinsa na dawo da zaman lafiya, tsaro da oda a Katsina.
KU KARANTA KUMA: Covid-19: Yadda muka ciyar da iyalai 127,588 lokacin kulle - Minista Sadiya
Ya yi kira ga rundunar sojin Najeriya da taimakon sauran hukumomin tsaro da suyi abunda za su iya domin fitar da yan bindigan.
Gwamnan ya ce:
“Wuraren da muke da matsala kawai sune kananan hukumomin Faskari, Sabwa da Dandume a jihar, a yankunan Jibia, Batsari, Safana da Danmusa an samu zaman lafiya.
“Daga rahotannin, da nake samu duk safe idan ka ga lamarin fashin shanu ko garkuwa da mutane toh yawacinsu a kewayen Faskari, Sabwa da Dandume ne. Muna ta kai wa hukumar soji korafi a kan su karbe ragamar yankunan Gurbi-Gidan Jaja-Kaura Namode na jihar Zamfara.
“Har sai an dawo da cikakken tsaro a wannan yankuna, kasancewarsu masu hatsari inda yawancin yan bindiga ke zama da yawo kai tsaye, idan ba haka ba, ba za mu iya kare Katsina ba ba tare da tsaro a Zamfara ba, saboda kaso 99 na dukkanin hare-hare da garkuwa da mutane da ke faruwa a Katsina daga Zamfara ne."
KU KARANTA KUMA: Akwai dalili: Budurwa ta rataye kanta a Kano
Sarakunan sun ce rashin tsaro, talauci, rashin ilimi da sauran kalubale, sune suke tabarbarar da ci gaban ilimin yara mata a jihohi irin Borno, Zamfara, Gombe, Sokoto da Kebbi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng