Covid-19: Yadda muka ciyar da iyalai 127,588 lokacin kulle - Minista Sadiya
- Ma’aikatar jin kai da walwala ta bayyana cewa ta ciyar da gidaje 127,588, a lokacin kullen annobar korona a kasar nan
- A cewar ma’aikatar, yaran makaranta da ake ciyarwa ne aka bi su har gida aka baiwa iyayensu kasonsu a lokacin kullen korona
- Ma’aikatar ta ce cikin kowane buhu da aka raba wa iyayen yara, akwai shinkafa, man gyada, manja, gishiri, timatir da wake
Ma’aikatar jin kai da walwala ta bayyana cewa ta canja tsarin shirin ciyar da dalibai a lokacin kullen korona, inda ta bayyana cewa ta ciyar da gidaje 127,588 da ke dauke da yaran makaranta da ke amfana daga shirin.
A bisa ga rahoton da ma’aikatar ta gabatarwa da majalisar dattawa a watan Oktoba, ta ce kowani buhu na dauke da shinkafa 5kg, wake 5kg, man gyda 500ml, man ja 750ml, gishiri 500g, timatirin gwangwani 140g da kwai guda 15.
An fara rabon kayayyakin ne a watan Mayun 2020, kuma an gudanar da rabon ne a birnin tarayya, jihohin Ogun da Lagas.
KU KARANTA KUMA: Addinin musulunci ya samu babban karuwa: Fastoci fiye da 42 da matayensu sun musulunta a Abuja (hotuna)
A cikin haka, gidaje 29,609 ne suka amfana a birnin tarayya, yayinda a Lagas gidaje 37,589 suka amfana.
Sannan a Ogun gidaje 60,390, gaba daya dai jimilar gidaje 127,588 ne suka ci moriyar shirin, jaridar Premium Times ta ruwaito.
“Gwamnatocin jihohi da ma’aikatar birnin tarayya ne suka yi rabon kayan abincin tare da hadin gwiwar shirin abinci na duniya, kungiyoyi masu zaman kansu sannan hukumar DSS da na ICPC suka sanya idanu a kai.
Koda dai rahoton bai bayar da bayani kan kalubalen shirin ciyarwar ta fannin kudi ba, ta ce duk a cikin shirin tallafinta na COVID-19.
KU KARANTA KUMA: Akwai dalili: Budurwa ta rataye kanta a Kano
An sakarwa ma’aikatar da kudi naira miliyan 551.4 a watan Yuni.
Tuni dai aka kashe kimanin naira miliyan 321.4 daga cikin wannan kudi da aka saki, inda a yanzu kimanin naira miliyan 230 ya yi saura a asusun ma’aikatar.
“Yana da matukar muhimmanci a lura cewa an kayyade aikin da za a yi da kudin da aka saki, cewa na tallafin ne a lokacin annobar korona,” in ji rahoton.
A wani labarin, wasu sarakunan Arewa sun nuna damuwa a kan tabarbarewar ilimin yara mata a wasu jihohin arewa guda biyar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sarakunan sun ce rashin tsaro, talauci, rashin ilimi da sauran kalubale, sune suke tabarbarar da ci gaban ilimin yara mata a jihohi irin Borno, Zamfara, Gombe, Sokoto da Kebbi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng