Zamfara: Matawalle ya jagoranci kubutar da 'yammata 26 da 'yan bindiga suka sace a Katsina

Zamfara: Matawalle ya jagoranci kubutar da 'yammata 26 da 'yan bindiga suka sace a Katsina

- Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da kubutar da wasu 'yammata 26 da 'yan bindiga suka sace tare da yin garkuwa da su a Zamfara

- Ceto 'yammmatan na daga cikin nasarorin da jihar Zamfara ta samu a cigaba da yin sulhu da 'yan bindiga

- Wannan ceto ƴammatan da aka yi yasa adadin mutanen da ƴan bindiga daɗi suka saka a Zamfara ya kai sama da arba'in 40 daga satin da ya gabata

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya ce kwalliya ta na biyan kuɗin sabulu a tattaunawar sulhun da ake yi da ƴanbindiga daɗi a jihar, sakamakon sakin ƴammata 26 ƴan asalin jihar Katsina wanda dukkan su yara matane masu ƙarancin shekaru.

An saki ƴammatan ga gwamnatin jihar Zamfara ba tare da biyan kuɗin fansa ba, a cewar Zailani Baffa, mai magana da yawun gwamna Matawalle.

An sace ƴammatan ne daga ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina, kuma an kawo su jeji cikin jihar Zamfara.

Sai cikin sa'a gwamnatin Zamfara ta samu nasarar ganosu tare da ceto su ta hanyar haɗinguiwa da ƴan bindigar, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Abubakar Dauran.

Kwamishinan ne ya wakilci gwamna Matawalle a tattaunawar sulhu da ƴan bindigar Zamfara a ƙoƙarin tabbatar da tsaro da kuma zaman lafiya a jihar.

Gwamna Matawalle, wanda ya karɓi kuɓutattun ƴan matan, ya ce gwamnatinsa ba zata yi watsi da tattaunawa da 'yan bindiga ba don hakan zai wanzar da zaman lafiya kamar yadda alamu ke nunawa.

KARANTA: Obasanjo ya fadi abinda ya rusa takarar Atiku lokacin da yaso bijire masa a 2003

Ya ƙara da cewa amfani da ƙarfin bindiga kaɗai ba shi zai kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga ba a jihar Zamfara.

Ya ce "wannan shine mahangar mu ta yin sulhu da ƴan bindigar , a tattauna tare da yin sulhu domin wanzuwar zaman lafiya a jihar Zamfara.

An ceto 'yammatan Katsina 26 daga hannun 'yan bindigar Zamfara
Matawalle da yammatan da aka kwato
Asali: Twitter

"Waɗanda suka yarda cewa bamu yi dai-dai ba da muka yi sulhu da ƴan bindigar, basu san cewa kuɓutar da ƴammatan ba karamar nasara ce marar misaltuwa ba".

KARANTA: Ba haka bane Farfesa; Shehu Sani ya ci gyaran Zulum a kan sababin fara yakin Boko Haram

"Ƴammatan 26 da aka ceto, wanda shekarunsu ke tsakanin 8 zuwa 12, an duba tare da tantance lafiyarsu kuma an basu sabbin kayan sawa," a cewar Matawalle.

Gwamnan ya bayar daumarnin a mayar da ƴammatan jihar Katsina.

Ceto ƴammatan ya kara adadin ƴammata da mutanen da aka ceto zuwa sama da arba'in daga makon da ya gabata.

Wata kotun tarayya a Abu Dhabi Dubai, ta yankewa ƴan Najeriya 6 (sunayensu) shidda hukunci bisa zarginsu da ɗaukar nauyin Boko Haram, kamar yaddaLegit.ng ta wallafa d sanyin safiyar ranar Litinin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel