Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai na cikin ganawar sirri da shugabannin tsaro

Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai na cikin ganawar sirri da shugabannin tsaro

- Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Wase na jagorantar wani taro da hukumomin tsaro na kasa

- Manyan jami’ai daga hukumomin tsaro daban-daban na wakiltan bangarorinsu

- Zuwa yanzu dai ba a san abunda tattaunawar nasu ya kunsa ba

Shugaban majalisar wakilai na cikin ganawar sirri tare da shugabannin hukumomin tsaro a kasar.

Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Wase ne ya jagoranci ganawar wanda aka fara da misalin karfe 2:15 na yau Litinin, 16 ga watan Nuwamba, jaridar Punch ta ruwaito.

An tattaro cewa an bukaci manema labarai da sauran mutane su fita daga cikin dakin taron a yayinda ake shirin fara ganawar.

KU KARANTA KUMA: Addinin musulunci ya samu babban karuwa: Fastoci fiye da 42 da matayensu sun musulunta a Abuja (hotuna)

Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai na cikin ganawar sirri da shugabannin tsaro
Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai na cikin ganawar sirri da shugabannin tsaro Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Manyan jami’ai daga hedkwatar tsaro, rundunar sojin Najeriya, rundunar sojin sama, rundunar sojin ruwa, rundunar yan sandan Najeriya, da rundunar tsaro na farin kaya (DSS) duk sun hallara.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da wakilai daga hukumar kula da shige da fice na kasa, hukumar gyara halayya ta kasa, da dai sauransu.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Katsina, Bello Masari, a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, ya koka kan ayyukan yan bindiga a jiharsa.

Masari, wanda ya yi magana da manema labarai a Kafur ya bayyana cewa mafi akasarin wadannan miyagun su kan je su haddasa tashin hankali a Katsina sannan su koma mabuyarsu a Zamfara, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Katsina, sun kashe na kashewa, sun kwaci makamai da dukiya

Gwamnan ya yi korafin cewa yan bindigan na yin duk abunda za su iya don wargaza kokarinsa na dawo da zaman lafiya, tsaro da oda a Katsina.

Ya yi kira ga rundunar sojin Najeriya da taimakon sauran hukumomin tsaro da su abunda za su iya domin fitar da yan bindigan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel