Akwai dalili: Budurwa ta rataye kanta a Kano

Akwai dalili: Budurwa ta rataye kanta a Kano

- Wata matashiyar budurwa ta rataye kanta a jihar Kano a gidan da take aiki

- Sai dai zuwa yanzu ba a san dalilinta na kashe kanta ba domin bata bar wasika da ke bayani kan hakan ba

- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin inda ta kaddamar da bincike

Wani rahoto da muke samu daga jaridar Punch ya nuna cewa wata matashiyar budurwa mai shekaru 16 a duniya mai suna Bahijja Gombe, ta kashe kanta a gidan da take aiki a Zoo Road, jihar Kano.

Rahoton ya nuna cewa Bahijja, wacce ta kasance yar asalin jihar Gombe ta kashe kanta ne ta hanyar rataya.

Sannan bata bar wani jawabi a rubuce ba wanda zai bayyana dalilinta na daukar wannan tsatsauran mataki na kashe kanta.

Wata majiya ta ce Bahijja, wacce ke aikin goge-gogen gida da kuma kula da masu siyayya a shagon uwargijiyarta, bata zuwa kowani makaranta.

KU KARANTA KUMA: Addinin musulunci ya samu babban karuwa: Fastoci fiye da 42 da matayensu sun musulunta a Abuja (hotuna)

Akwai dalili: Budurwa ta rataye kanta a Kano
Akwai dalili: Budurwa ta rataye kanta a Kano Hoto: @vanguardngrnews
Asali: UGC

Majiyar ta ce an tsinci gawarta a cikin wani daki a ranar Asabar da misalin karfe 10:00 na dare, inda ta kara da cewa mazauna yankin na daman zargin akwai wata a kasa.

Kakakin yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna, ya tabbatar da afkuwar al’amarin, ya bayyana cewa an tsinci gawar matashiyar a rataye a cikin gidan.

Ya bayyana cewa tuni aka dauke gawarta zuwa wajen ajiye gawarwaki na asibitin murtala sannan kuma cewa rundunar yan sandan ta fara gudanar da bincike a kan al’amarin domin gano musababbin mutuwarta.

A wani labari na daban, mun ji cewa an shiga halin fargaba a jihar Kano bayan kisan wasu mutane biyu da ake zargin yan sandan da ke yaki da yan daba a jihar da aikatawa.

An tattaro cewa an harbe matasan ne a unguwar Sharada lokacin da sashin yaki da yan daba suka ziyarci yankin.

Wani rahoto da ba a tabbatar ba ya nuna cewa yan sandan kan matsa wa matasa a yankin amma sai aka samu tirjiya a wannan rana ta Asabar wanda ya yi sanadiyar bude wuta da mutuwar mutum biyu.

KU KARANTA KUMA: Ilimin ƴaƴa mata: Hankalin Sarakunan Arewa ya tashi kan wasu jihohi 5

Matasan da aka kashe sune Abubakar Isah da Ibrahim Sulaiman (Mainasara) jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel