Tsegumi da nishaɗi: Amaryar hadimin Buhari ta aikewa mijinta Bashir Ahmad zafafan kalamai

Tsegumi da nishaɗi: Amaryar hadimin Buhari ta aikewa mijinta Bashir Ahmad zafafan kalamai

- Amaryar hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ta aike masa kalamai masu motsa zuciya

- Na'ema ta yi hamdala ga Allah da ya mallaka mata Bashir a matsayin abokin rayuwarta

- Ta jadadda cewa ko sau nawa za a dawo shi din za ta zaba a matsayin mijinta ba tare da kokwanto ba

Tabbass soyayya ruwan zuma ce musamman idan mutum ya yi dace da muradin ransa, kuma masoyinsa na hakika.

Duk da cewar ba a rasa sabani a zamantakewa na ma’aurata musamman duba ga karin maganar nan da Hausawa kan yin a cewa ko a tsakanin harshe da hakori ana sabawa.

Sai dai mafi akasarin ma’auratan da suka san kansu, su kan yi duk wani kokari don ganin cewa rayuwar aurensu ya tafi cikin jin dadi da walwala ba tare da bayar da kafar da wani zai shigo ciki ba.

KU KARANTA KUMA: Kudirina na gaba shine na zama fasto ko Shugaban kasar Nigeria, in ji Fayose

Tsegumi da nishaɗi: Amaryar hadimin Buhari ta aikewa mijinta Bashir Ahmad zafafan kalamai
Tsegumi da nishaɗi: Amaryar hadimin Buhari ta aikewa mijinta Bashir Ahmad zafafan kalamai Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Musamman masu iya magana kan ce namiji dan tarairaya ne, ya kan so mace da ta san kan soyayya sannan ta dunga bashi kulawa a koda yaushe, kuma a duk sanda ta samu damar hakan.

A cikin haka dai ba a bar amaryar hadimin Shugaban kasa, Bashir Ahmad wato Na’ema a baya ba wajen nuna wa duniya irin son da take yi wa mijin nata.

A wani wallafa da ta yi a shafinta na Twitter, Na’ema ta aikewa mijinta Bashir Ahmad zafafan kalamai masu motsa zuciyar ma’abota soyayya.

Ta yi godiya ga Allah Ubangiji da ya mallaka mata shi a matsayin mijinta yayinda ta bayyana cewa ko sau nawa za a dawo shi dinne za ta zaba a matsayin abokin rayuwarta.

Ta wallafa a shafin nata kamar haka: "Alhamdulillah ya Allah, Alhamdulillah da ka bani @BashirAhmaad. Ko a gaba kai zan zaba na sake zaba, ba tare da nazari ba kuma ba tare da kokwantoba, zan ta zabarka ya masoyina."

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: ‘Yan bindiga sun sace malamin kwalejin Nuhu Bamalli da yara 2 a Zariya

A wani labarin, wata jarumar fina-finan Nollywood, Olive Utalor ta yi ikirarin mallakar duk wani abu da zai karkato da hankalin namiji a aure.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel