Wata sabuwa: ‘Yan bindiga sun sace malamin kwalejin Nuhu Bamalli da yara 2 a Zariya
- Yan bindiga sun kai mamaya sashen gidajen malamai a makarantar kimiya da fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya
- Maharan sun sace malami daya da kuma yara biyu sannan suka harbi wani
- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin inda tace a yanzu haka ta baza jami'anta domin ceto wadanda aka sace
Yan bindiga a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba, sun kai farmaki kwatas din malamai na kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli Polytechnic da ke Zariya sannan suka sace wani lakcara da yara biyu, sannan suka harbi wani mutum daya.
An tattaro cewa wanda aka harban yana nan yana jinya a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello.
Da aka tuntube shi, jami’in hulda da jama’a na makarantar, Abdallah Shehu, ya ce yana cikin wani taro sannan ya yi alkawarin kira da zaran ya gama, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Nasarun Minallah: Sojin Nigeria sun farmaki ISWAP, sun cafke masu haɗa makamin IEDs
Sai dai kuma, rundunar yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da lamarin cewa ya afku ne da misalin karfe 10:00 na dare, ta kara da cewa an garzaya da wanda ya ji rauni zuwa asibitin koyarwa na ABU don jinya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige ya ce: “Muna kan lamarin. Yan sanda sun kakkabe yankin gaba daya sannan suna kokarin ceto mutanen.”
KU KARANTA KUMA: EndSARS: Kuna da makonni 2 don yin bincike a kan Sam Adeyemi da sauransu, kotu ga yan sanda
A wani labari na daban, rundunar sojin sama ta Operation Thunder Strike ta samu nasarar kashe wasu 'yan ta'adda da suke dauke da miyagun makamai.
Rundunar sojin saman sun hangi 'yan ta'addan ta wata na'ura mai hangen nesa, inda suka hangi 'yan ta'addan a kauyen Kaboru, suna tunkarar dajin Kwiambana.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng