Da ɗuminsa: Kwamishinan lafiya na Benue, Emmanuel Ikwulono ya mutu
- Allah ya yiwa kwamishinan lafiya na jihar Benue, Dr Emmanuel Ikwulono, rasuwa
- An tattaro cewa an yi wa Ikwulono tiyata na wani rashin lafiya da ba a bayyana ba, amma sai abun ya zo da matsala wanda ya kai ga mutuwarsa
Wata majiya ta gidan gwamnatin jihar ta tabbatar da mutuwar nasa
Kwamishinan lafiya na jihar Benue, Dr Emmanuel Ikwulono, ya rasu, Nigerian Tribune ta ruwaito.
A ranar 5 ga watan Agustan 2020 ne aka rantsar da Dr Ikwulono a matsayin kwamishinan lafiya da harkokin jama’a na jihar Benue.
Ya maye gurbin Dr Sunday Ongbabo wanda ya yi murabus daga majalisar zartarwa ta jihar.
KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Kotu ta garƙame wasu mata biyu da laifin yunƙurin kashe gwamna Oyetola
Wata majiya ta gidan gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa kwamishinan wanda aka ba gado a asibiti ya mutu sakamakon rashin nasara da aka samu a aikin tiyata da aka yi masa na wani ciwo da ba a bayyana ba.
“Ya halarci zaman majalisar zartarwar jihar da aka gudnar na karshe a makon da ya gabata sannan ya je aka yi masa aiki.
“Mutuwarsa ya zo kamar almara a yammacin nan,” in ji majiyar gwamnatin.
A gefe guda, mun ji cewa tsohon gwamnan Jihar Kaduna Abdulkadir Balarabe Musa.
Tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani shima ya sanar da rasuwar tsohon gwamnan a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 11 ga watan Nuwamba.
KU KARANTA KUMA: Jihar Kaduna na alfahari da Balarabe Musa – Elrufai
A sakon da ya wallafa a Twitter, Shehu Sani ya rubuta "Alhaji Balarabe Musa ya rasu a yau. Allah ya jikan rai ya kuma saka masa da gidan Aljanna Firdausi. Amin."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.n
Asali: Legit.ng