Kudirina na gaba shine na zama fasto ko Shugaban kasar Nigeria, in ji Fayose

Kudirina na gaba shine na zama fasto ko Shugaban kasar Nigeria, in ji Fayose

- Tsohon gwanan Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana wasu burika biyu da yake muradin cikawa a nan gaba

- Fayose ya ce yunkuri na gaba da yake son yi a rayuwarsa shine ya zama fasto ko kuma shugaban kasar Najeriya

- Ya ce ta hanayar zama mai isar da sakon Ubangiji ne kadai zai saka wa Allah kan ni'imomin da yayi masa a rayuwa

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, wanda ya cika shekaru 60 a yau Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, ya ce kudirinsa na gaba shine imma ya zama fasto ko kuma Shugaban kasar Najeriya.

Fayose ya yi magana ne a tashar radiyo ta Ekiti wato People’s FM, (104.19) kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito.

Sai dai kuma, tsohon gwamnan bai bayar da ainahin lokacin da zai nemi cika wadannan kudiri nasa ba, ko kuma wanne ne zai fara nema.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: ‘Yan bindiga sun sace malamin kwalejin Nuhu Bamalli da yara 2 a Zariya

Ya ce Allah ya yi masa ni’imomi da yawa, don haka, hanyar da ta fi dacewa ya bi don gode yin godiya ga abubuwan da Ubangiji ya yi masa shine yin aikin Allah.

Kudirina na gaba shine na zama fasto ko Shugaban kasar Nigeria, in ji Fayose
Kudirina na gaba shine na zama fasto ko Shugaban kasar Nigeria, in ji Fayose Hoto: @ayofayose
Asali: UGC

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa ya yafe wa dukkanin mutanen da suka yi masa ba daidai ba, a yayinda yake kujerar mulki da bayan ya sauka.

Ya yi korafin cewa mutane da dama da ya aminta da su sannan ya daukaka su sun yasar da shi domin zama hadiman abokan hamayyarsa a siyasa, bayan ya bar karagar mulki.

Fayose ya kuma yi watsi da rade-radin cewa yana zawarcin zama sanata.

KU KARANTA KUMA: Nasarun Minallah: Sojin Nigeria sun farmaki ISWAP, sun cafke masu haɗa makamin IEDs

Ya ce ya tsani zama sanata wanda ke kafa dokoki da bangaren zartarwa ba za ta aiwatar ba.

A ranar Asabar, tsohon gwamnan ya wallafa wani hoto na takarar siyasarsa ta farko da kuma yadda ya fara lamarin siyasarsa a shafin Twitter.

A wani labarin, wata kotun majistare da ke Abuja ta umurci rundunar yan sanda a birnin tarayya da ta binciki lamuran da ake zargin Sam Adeyemi, Aisha Yesufu da sauransu da hannu a ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng