Na mallaki duk abinda namiji zai bukata, na killace masa budurcina - Jaruma Fim Utalor

Na mallaki duk abinda namiji zai bukata, na killace masa budurcina - Jaruma Fim Utalor

- Babban abu mai wahala a zamanin nan shine samun cikakkiyar budurwa, sabuwa dal a leda, kuma samun hakan yana da dadi

- Jarumar fina-finan Nollywood, Olive Utalor, ta ce tana matukar alfaharin adana budurcinta har sai daren farkon aurenta

- Ta ce mijinta zai yi alfahari da ita, saboda ta killace kanta, kuma tana da duk wasu abubuwa da za su karkato da hankalinsa gareta

Wata jarumar fina-finan Nollywood, Olive Utalor ta yi ikirarin mallakar duk wani abu da zai karkato da hankalin namiji a aure, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Jaruma Utalor ta fadi hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da ita, inda ta tabbatar da yadda ta adana budurcinta har sai daren aurensu na farko. Ta kara da cewa, ta tabbatar da yadda mijinta zai yi alfahari da ita, ta yadda ta adana budurcinta har aure.

A cewar jarumar; "Mijina zai yi alfahari da yadda na adana budurcina har sai da muka yi aure. Idan kun lura, ina da duk wasu abubuwa da za su dauki hankalin namiji.

"Duk da dai na fuskanci kalubale wurin adana budurcina har zuwa yanzun. Bana tsoron aure, saboda na daura dammarar fuskantar ko wanne irin kalubale.

"Idan na dage a kan abu, ina karkatar da duk hankalina ne a kan shi. Aure tarayya ce tsakanin mutane biyu masu kaunar juna, masu burin dagewa wurin fuskantar duk wani kalubale tare. Babu wani abinda zai dagamin hankali. Nasan aurena mai daurewa ne."

KU KARANTA: Kotu ta bukaci a garkame mata wasu mutum 2 da suka yi yunkurin kashe Gwamna

Na mallaki duk abinda namiji zai bukata, na killace masa budurcina - Jaruma Fim Utalor
Na mallaki duk abinda namiji zai bukata, na killace masa budurcina - Jaruma Fim Utalor. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: An sallami 'yan sanda 10 daga aiki a jihar Legas

A wani labari na daban, Sanata Ali Ndume ya zargi tubabbun 'yan Boko haram bai wa 'yan ta'addan bayanai a kan sojoji, musamman bayan ganin harin da suka kai Damboa kwanan nan.

Ndume, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar tarayya ta sojoji, ya sanar da hakan lokacin gabatar da kasafin sojoji a gaban kwamitin, ranar 11 ga watan Nuwamba.

Ndume ya yi amfani da damar, inda yace wajibi ne gwamnatin tarayya ta soke shirin taimakonsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel