IPMAN ta umurci gidajen mai su fara sayar da mai a farashin N170

IPMAN ta umurci gidajen mai su fara sayar da mai a farashin N170

- Farawa da iyawa, gidajen mai zasu fara sayar da fetur a sabon farashi

- Daga hawan shugaba Buhari ya mulki a 2015, farashin litan mai ya tashi daga N87 zuwa N170 yanzu

- Yan Najeriya suna kira ga gwamnatin ta tausaya wa al'umma

Kungiyar yan kasuwar mai masu zaman kansu IPMAN, shiyar jihar Kano, ta umurci mambobinta masu gidajen mai dake yankin Arewa maso yamma su fara sayar da mai a farashin N168 zuwa N170 ga lita.

Shugaban IPMAN na Kano, Bauchi, Jigawa, da Katsina, Bashir Dan-Mallam, ya bada umurnin hakan yayin hira da manema labarai ranar Juma'a.

A cewarsa, kungiyar ta bi umurnin PPMC ne da ya kara farashin litan man fetur.

"Ina kira ga mambobin dake karkashin shiyarmu su aiwatar da karin farashin ba tare da bata lokaci ba daga N160 zuwa N168-N170 ga lita, " yace.

"Mun yanke shawaran haka ne bayan samun sako daga PPMC, inda suka bamu shawaran kara farashin man fetur a watan Nuwamba, 2020."

Ya tabbatarwa al'umma cewa ba za ta yi kasa a gwiwa wajen samar da isasshen man fetur a sassan jihohin da kewaye ba.

KU KARANTA: Gwamnatin Kogi ta sanya haraji kan kowane burodi a jihar

IPMAN ta umurci gidajen mai su fara sayar da mai a farashin N170
IPMAN ta umurci gidajen mai su fara sayar da mai a farashin N170 Hoto: Oando
Asali: UGC

KU KARANTA: Burodi ya shiga jerin abincin manya irinsu Shinkafa da Albasa, Shehu Sani

Mun kawo muku cewa, yan Najeriya su shirya hauhawar farashin man fetur saboda sabon farashin jigilar mai a Depot da kamfanin PPMC ta kara daga N147.67 zuwa N155.17.

Farashin man yanzu na iya tashi zuwa N170 da lita a gidajen mai a fadin tarayya.

A takardar da kamfanin PPMC ta saki ranar Alhamis, 11 ga Nuwamba, an gano cewa za'a fara sayar da mai a wannan farashin ranar 13 ga Nuwamba, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel