Burodi ya shiga jerin abincin manya irinsu Shinkafa da Albasa, Shehu Sani

Burodi ya shiga jerin abincin manya irinsu Shinkafa da Albasa, Shehu Sani

- Dan fafutuka, Shehu Sani, ya yi tsokaci kan tasirin da harajin da aka daura kan burodi zai yiwa al'ummar jihar Kogi

- Sani ya ce yanzu Burodi zai shiga jerin kayan abinci masu tsada sakamakon haka

- Har yanzu yan Najeriya na kuka kan hauhawar farashin shinkafa

Har wa yau, sanya kudin haraji kan Burodi a jihar Kogi na cigaba da fuskantar suka daga wajen yan Najeriya.

Daya daga cikin wadanda sukayi tsokaci kan lamarin shine tsohon Sanata, Shehu Sani, wanda ya bayyana cewa wannan haraji zai sabbaba hauhawar farashin Burodi.

Shehu Sani ya ce Burodi zai shiga jerin abincin alfarma a jihar Kogi.

Sanata Shehu a maganar da yayi ranar Juma'a 13 ga Nuwamba ta shafinsa na Tuwita, ya bayyana cewa Burodi zai fara tsada a jihar Kogi, kaman shinkafa da albasa.

KU KARANTA: Wannan rashin tausayi ne - IPMAN ta yi Alla-wadai da karin farashin mai zuwa N170

Burodi ya shiga jerin abincin manya irinsu Shinkafa da Albasa, Shehu Sani
Burodi ya shiga jerin abincin manya irinsu Shinkafa da Albasa, Shehu Sani Hoto: Credits: Pulse Nigeria/Business Day
Asali: UGC

Mun kawo muku cewa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.

Amma, kungiyar masu gasa burodi reshen jihar sun bayyana cewa basu goyon harajin.

Wani jigo a kungiyar wanda aka sani da Godfirst ya ce suna shirye shiryen yadda zasu zauna da masu alhakin karbar kudin.

KU KARANTA: Farashin man fetur zai tashi N170 yayinda aka kara kudin Depot zuwa N155

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel