Zan ci gaba da aure aure har sai na samu wanda ya dace da ni, in ji bazawara mai aure 10

Zan ci gaba da aure aure har sai na samu wanda ya dace da ni, in ji bazawara mai aure 10

- Bazawara mai aure goma ta fito neman mijin da za ta sake aura ko za a dace

- A cewar matar mai shekaru 56 ta kan fita daga gidan aurenta da zaran ta ga wani abu da ba za ta iya lamunta ba

- Hujjar da ta bayar na barin wasu daga cikin tsoffin mazajenta shine cewa ba sa nuna mata soyayya yadda take nuna masu

Wata bazawara da ta fita daga gidan mijinta bayan aure sau 10, ta bayyana cewa har yanzu bata yanke kauna daga kara aure ba har ta samu miji nagari da ya dace da ita wanda za su yi soyayya har mutuwa.

Matar mai shekaru 56 ta shaida wa sabon bazawarinta mai suna Dokta Phil, cewa ta rabu da mazajenta na baya ne saboda ba ta samu wanda ya dace da ita ba.

“Idan har na yi aure na ga abu bai yi min ba, kuma ba zan lamunta ba, zan kasance ta farko in bayyana wa mijina cewa ya sake ni don mu rabu,” inji ta.

Matar mai suna Cassey ta kasance ’yar kasuwa kuma ’yar kasar Amurka wacce ta samu nasarori a harkokin kasuwancinta.

KU KARANTA KUMA: An kama wani malamin makaranta da ya yi garkuwa da dalibinsa

Zan ci gaba da aure aure har sai na samu wanda ya dace da ni, in ji bazawara mai aure 10
Zan ci gaba da aure aure har sai na samu wanda ya dace da ni, in ji bazawara mai aure 10 Hoto: Indo Canada Education Council
Asali: UGC

A yanzu da take shirin ganin ta sake samun wani da za ta aura, bazawarar ta ce ba ta damu ko sau nawa ta yi aure tana fita daga gidajen mazajen ba, cewa ba za ta daina neman aure ba har sai ta samu wanda zai rike ta da soyayya har abada.

Ta bayyana wa Dokta Phil cewa, aurenta na farko ta zauna a gidan aure na tsawon shekara takwas sannan suka rabu cikin mutunci.

Sannan a aurenta na biyu ta yi zaman aure ne na shekara bakwai da kuma yin baiko na shekara biyu da rabi, inda suka haihu.

Ta ce amma sun fara samun matsala ce lokacin da mijinta ya daina furta mata kalaman soyayya.

A cewarta a duk lokacin da ta furta wa mijin kalmar soyayya, sai ya mayar mata ba yadda ta furta masa ba, jaridar Aminiya ta ruwaito.

Sai dai Cassey ba ta yi cikakken bayani kan yadda ta rabu da mazan da ta aura daga na uku zuwa na goma ba.

Ta auri maza iri-iri wadanda suka hada da mai sha’awar shagaltuwa da mai son yin wa’azi, kuma tun tana kwaleji take neman wanda ya dace da ita da za su yi zaman aure amma ba ta samu ba, kamar yadda ta bayyana wa Dokta Phil.

KU KARANTA KUMA: Dogarin Gwamna Obaseki ya yanke jiki ya fadi a wajen bikin rantsar da shi (bidiyo)

Sai dai a cewar sabon bazawarin Cassey, zai kasance maigidanta wanda zai bar mata tarihi, yana kiran ta da sunan mai ba da umarni game da abin da take so.

Cassey ta kara da cewa, duk da rashin cika alkawarin da ake yi mata game da soyayyar da ake yi mata, ba za ta daina neman wanda zai rike ta da gaskiya da amana ba.

A wani labarin, wani ma'aikacin banki, mai suna Rowland Ogunebo, ya maka matarsa, Blessing, a kotun Ile-Tuntun da ke Ibadan saboda shigar banza da kuma bin maza.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel