An kama wani malamin makaranta da ya yi garkuwa da dalibinsa

An kama wani malamin makaranta da ya yi garkuwa da dalibinsa

- Yan Sandan a Jihar Ogun sun cafke wani malami, Odugbesan Ayodele, bisa zargin garkuwa da dalibinsa mai shekaru takwas

- Malamin ya sace yaron sannan kuma ya nemi kudin fansa N200,000 daga mahaifiyarsa

- An yi nasarar kama shi ne bayan mahaifiyar yaron ta kai karar batan dan nata ofishin yan sanda da kuma kiran da aka mata na neman kudin fansa

Rundunar yan sanda ta kama wani malami bisa laifin garkuwa da wani tsohon dalibinsa mai shekaru takwas a yankin Akute da ke jihar Ogun, Channels TV ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda a jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, cewa an kama wanda ake zargin, Odugbesan Ayodele, mai shekaru 29 a ranar Laraba na makon da ya gabata.

Ya yi bayanin cewa kamun nasa ya biyo bayan wani korafi da mahaifiyar yaron da aka sace, Fatimat Akeeb ta kai hedkwatar yan sanda na Ajuwon, cewa danta ya tafi makaranta a Arifanla da ke Akute amma bai dawo ba har karfe 6:00 na yamma.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: IGP ya buƙaci N24.8bn domin sayen fetur wa motoci da baburan ƴan sanda

An kama wani malamin makaranta da ya yi garkuwa da dalibinsa
An kama wani malamin makaranta da ya yi garkuwa da dalibinsa Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

A cewar Oyeyemi, mahaifiyar yaron ta samu kiran waya daga wani mutum da bata sani ba inda ya bukaci ta shirya biyan N200,000 idan tana son ganin danta a raye.

Ta bayyana cewa wanda ya kira ta din ya fada mata cewa wani ne ya kawo masa yaron kuma ba zai sake shi ba har sai an biya kudin da ya ce.

“Da samun rahoton, DPO na yankin Ajuwon, SP Andrew Akinseye, ya umurci jami’ansa da su fara bincike wanda ya yi sanadiyar gano mabuyarsu.

“Don kar a cutar da yaron, an yaudari wanda ake zargin tare da biyan wani kaso na fansan sannan daga baya aka cafke shi ya kai ’yan sanda inda ya ajiye yaron wanda aka ceta ba tare da rauni ba.

“Da aka tambaye shi, ya amsa laifinsa amma ya daura laifin kan aikin shaidan,” cewar sanarwar.

KU KARANTA KUMA: Ana wata ga wata: Sabuwar cuta ta ɓulla a Nigeria, ta kashe 17 a Benue

A martaninsa, kwamishinan yan sandan Ogun, Edward Ajogun, ya yi umurnin tura mai laifin zuwa ga shashin yaki da masu garkuwa da mutane don ci gaba da bincike da kuma hukunta shi.

Ya kuma roki iyaye da su dunga lura da duk wani motsi na yaransu a yayin zuwa da tasowa daga makaranta domin kada miyagu su samu galaba a kansu.

A wani labarin, Shugaban karamar hukumar Guma da ke jihar Benue, Caleb Aba, ya sanya dokar kulle na sa’o’i 12 a garin Daudu kan zargin satar al’aurar mutane da ya yawaita.

Garin Daudu wanda ke a hanyar babbar titin Makurdi-Lafia ya fuskanci tashin hankalin daga matasa kan zargin satar al’aurar mutane da ake zargin wasu mazaje da yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng