Miji ya maka matarsa a kotu a kan shigar banza da take
- Wani mutum mai suna Rowland ya maka matarsa a kotu saboda idan za ta fita tana yin shigar banza
- Rowland ya ce, idan ya umarceta da ta yi gaggawar canja kaya sai ta yi ta auna masa zagi
- A cewar matar, mijinta ba wayayye bane, shiyasa ba ya yaba wa shigarta mai cike da kayatarwa
Wani ma'aikacin banki, mai suna Rowland Ogunebo, ya maka matarsa, Blessing, a wata kotun Ile-Tuntun da ke Ibadan ranar Alhamis saboda shigar banza da kuma bin maza, The Nation ta wallafa.
Ogunebo, mazaunin Kasumu Estate da ke Ibadan, ya yi magana a kotun, inda yace: "Bazan iya cigaba da zama da blessing ba. Saboda ba ta mutunta 'yan uwana.
"Ba ta yin shiga irin ta matan aure. Tana saka guntayen buje da matsattsun riguna.
"Idan na umarceta da ta canja kayan, sai ta yi ta aunomin zagi," a cewarsa.
Blessing ta yi kokarin kare kanta a gaban kotu, inda tace: "Ina son mijina saboda muna da yara har 2 tare. Mijina baya son yadda nake shiga saboda ba wayayye bane."
Mai shari'ar, Chief Henry Agbaje, ya dage sauraron shari'ar har sai ranar 3 ga watan Disamba domin ma'auratan su gabatar da gamsassun hujjoji. Sannan ya shawarcesu da kada su dauki wani hukunci a hannayensu.
KU KARANTA: Ana barazana ga rayuwata saboda mutuwar aurena, Tsohuwar matar Sarki
KU KARANTA: Budurwa ta bayyana barnar da tayi wa saurayinta bayan ta gano zai auri wata
A wani labari na daban, an harbe wata alkalin kotu a kasar Philippines, a cikin harabar kotun da take alkalanci a birnin Manilla. Alkalin ta rasu bayan wani dan lokacin, sakamakon raunukan da ta samu saboda harbin.
Bayan 'yan sanda sun yi bincike, sun gano cewa akawun kotun, Amador Rebato, ne ya harbe alkalin mai suna Theresa Abadilla, daga bisani ya kashe kansa da kansa.
Har yanzu dai ba a samu wani bayani a kan dalilin da yasa akawun ya harbe alkalin ba.
Sai dai kafafen yada labarai na kasar, sun ruwaito yadda aka yi ta kashe masu shari'a da dama, inda Abadilla ce mutum ta 51 da aka kashe tun bayan hawa mulkin shugaba Rodrigo Duterte a 2016.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng