Ana tuhumar ma'aikaciyar jinya a kotu bisa zargin kashe jarirai 8

Ana tuhumar ma'aikaciyar jinya a kotu bisa zargin kashe jarirai 8

- Wata malamar asibiti da ke aiki da bangaren haihuwa na wani asibiti da ke gabashin garin Warrington

- Tun kimanin shekaru uku da suka gabata aka fara bincike a kan yawaitar mace-macen jarirai a asibitin

- Bayan tuhumarta da kisan kai, ana tuhumar Ungozomar mai suna Lucy da laifin yunkurin aikata kisan kai har sau goma

Wata ma'aikaciyar jinya ta gurfana a gaban wata kotun kasar Birtaniya bisa zarginta da kashe jarirai takwas (8) a ɓangaren karɓar haihuwa a asibiti.

Ungozuma Lucy Letby ta gurfana a gaban kotun majistare a arewa maso gabashin garin Warrington.

Ana tuhumar Ungozomar mai shekaru 30 da kashe rayuka har takwas. Dukkanin waɗanda ta kashe jarirai ne ƴanƙasa da shekara guda.

Har wa yau, an kara zarginta da yunƙurin kisa har sau goma, daga watan Yunin shekarar 2015 zuwa watan Yunin shekarar 2016, lokacin da ta ke aiki a asibitin Countess Of Chester a arewa maso kudancin birnin Chester.

DUBA WANNAN: Muhimman hanyoyi 5 da mulkin Biden zai amfani Nigeria da nahiyar Afrika

An dai fara binciken sababin mace-macen da ke afkuwa a ɓangaren karɓar haihuwar na asibitin tun shekaru uku da suka gabata.

Ana tuhumar ma'aikaciyar jinya a kotu bisa zargin kashe jarirai 8
Ana tuhumar ma'aikaciyar jinya a kotu bisa zargin kashe jarirai 8 @Thenation
Asali: Twitter

Letby ta yi magana a kotu don kawai a tabbatar da sunanta,kwanan watan haihuwarta da inda take zaune.

DUBA WANNAN: Hukumomi 428 ba zasu iya biyan albashin watan Nuwamba ba; FG ta ankarar da ma'aikata

Alƙalin gunduma, mai Shari'a Nicholas Sanders, ya ce za'a tura batun shari'ar zuwa ga babbar kotun Chester sannan Letby zata gurfana ranar juma'a.

Za'a cigaba da tsare Letby har zuwa zaman sauraron ƙarar na gaba.

A bangare guda, Legit.ng ta rawaito cewa Sanatoci sun bukaci gwamnatin tarayya ta yi koyi da takwararta Haɗaɗɗiyar daular Larabawa, UAE, wajen zaƙulo masu ɗaukar nauyin Boko Haram a Najeriya don ɗaukar matakin ladabtarwa da gaggawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel