Muhimman hanyoyi 5 da mulkin Biden zai amfani Nigeria da nahiyar Afrika

Muhimman hanyoyi 5 da mulkin Biden zai amfani Nigeria da nahiyar Afrika

- Sanata Joe Biden ne ya zama zakara a zaben shugaban kasar Amurka da aka yi ranar Talata, 3 ga wata

- Masu nazarin siyasar duniya na ganin cewa mulkin Joe Biden zai amfani Najeriya da saurn kasashen nahiyar Afrika

Bayan Joe Biden ya zamanto zakaran da ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka,wani rahoto da jaridar Quartz Africa ta wallafa, ya yi hasashen yadda gwamnatin Biden zata canja alaƙar Amurka da Nahiyar Afirka bakiɗaya.

Legit.ng Hausa ta kalato muku wasu daga cikin abubuwan da rahoton ya ƙunsa.

1. Zai ƙara danƙon alaƙarsu da Afirka.

Rahoton yayi nuni da cewa akwai yiwuwar Biden ya aro tunanin Trump na ganin ƙasar Sin(China)a matsayin abokiyar karawarsu a nahiyar Afirka.Wannan zai janyo ƙasar Amurka ta ƙara mu'amala da Afirka don ganin ta zarce China.

2. Ɓunƙasa ɗaukar nauyin kuɗaɗe

Acewar rahoton wataƙila Biden zai iya aringizon biyan kuɗaɗen baya da ba'a biya don tsaren tsaren da suka shafi cigaban Afirka.

Sabuwar gwamnati mai zuwa na iya dakatar da tsarin da hana Amurka ware kuɗaɗe don yin tsare-tsaren cigaba da bunƙasawa a Afrika.

3. Goyawa Ngozi Okonjo-Iweala don ganin ta shugabanci ƙungiyar kasuwanci ta duniya(WTO)

Daga cikin yunƙurin da ake hasashen gwamnatin Biden zata yi shine marawa tsohuwar ministar kuɗin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala, baya don ganin ta ɗare kujerar shugabancin WTO.

Hanyoyi guda biyar muhimmai da gwamnatin Biden zata yi ya shafi Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.
Joe Biden
Asali: UGC

Ngozi Okonjo-Iweala dai ta samu goyon bayan ƙasashen Turai (European union), Ƙasashen Afirka, da manyan ƙasashen Asiya irinsu Japan da china da sauransu.

Da tuni an sanar da sunanta a matsayin shugabar WTO, amma kasancewar kasar Amurka ƙarkashin shugaba Trump na goyin bayan wata ƴar takarar ya kawo cikas.

A ƙarƙashin Biden, Amurka na iya goyawa Ngozi Okonjo-Iweala baya.

4. Shiga ƙawancen samar da rigakafin Korona.

Amurka a ƙarƙashin shugaba Trump taƙi yarda ta shiga tsarin samar da allurar rigakafin Korona (COVAX). An ƙirƙiri tsarin ne don tabbatar da wadatuwa da rarraba alluran rigakafin yadda ya dace da zarar an samar da ita.

Biden na iya shiga tsarin idan ya karɓi gwamnati.

Idan har Amurka ta karɓi tsarin, za'a samu ƙarin kuɗaɗe wanda daga bisani ƙasashen Afirka da sauran ƙasashen duniya zasu ci moriya.

5. Zai hana Amurka janyewa daga ƙungiyar lafiya ta duniya WHO

A matsayin Amurka na ƙasar da tafi kowacce bada gudunmuwar kuɗi da taka rawa a ƙungiyar WHO, ficewarta ba ƙaramin girgiza al'amurran ƙungiyar zai yi ba. Kuma hakan zai fi shafar nahiyar Afrika, tunda ayyukan ƙungiyar nada muhimmanci sosai a nahiyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel