Ku daina yafewa mayakan kungiyar Boko Haram, ku yi koyi da kasar UAE; Majalisa ga FG
- Majalisa ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin yafewa mayakan kungiyar Boko Haram
- A cewar majalisar, sam bai kamata ake kyautatawa mayakan kungiyar Boko Haram ba duk da irin barnar da suka tafka
- Shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da rundunar soji, Sanata Ali Ndume, ya ce tubabben dan Boko Haram ne ya zama silar mutuwar kanal D. C Bako
Sanatoci sun bukaci gwamnatin tarayya ta yi koyi da takwararta Haɗaɗɗiyar daular Larabawa, UAE, wajen zaƙulo masu ɗaukar nauyin Boko Haram a Najeriya don ɗaukar matakin ladabtarwa da gaggawa.
Sun kuma yi kira ga rundunar sojin Najeriya da ta tayi watsi bawa tubabbun ƴan Boko Haram kariya waɗanda suke da hannu dumu dumu wajen kisan kiyashi da lalata dukiyar al-umma,inda suka ce tsarin kwata kwata ba dai-dai bane.
Da yake magana da ƴan jaridu jim kaɗan bayan ganawar sirri da shugaban rundunar Soji,Janaral Yusuf Buratai akan shawarwarin kasafin kuɗin tsaro na shekarar 2021,shugaban kwamitin Sanatoci akan rundunar Soji, Sanata Ali Ndume, ya ce ƙasar UAE ta yi aiki mai kyau.
KARANTA: Hukumomi 428 ba zasu iya biyan albashin watan Nuwamba ba; FG ta ankarar da ma'aikata
A farkon makon nan ne kasar UAE ta ɗaure waɗanda ake zargi da ɗaukar nauyin Boko Haram, inda yace ana jan ciki wajen yankewa masu irin wannan laifi hukunci a Najeriya.
Ya ƙara da cewa bawa tubabbun ƴan Boko Haram kariya na iya kawo naƙasu a yaƙin da ake da ta'addanci.
Kiran a zaƙulo sannan a gurfanar da masu ɗaukar nauyin Boko Haram yazo ne bayan an ɗaure ƴan asalin Najeriya Shida 6 a Haɗaɗɗiyar daular Larabawa Dubai bisa ɗaukar nauyin Boko Haram.
KARANTA: Arewa: Akwai maciya amana a cikin sojoji; rundunar soji ta koka
Ndume ya ce; "muna yabawa gwamnatin UAE kuma har yanzu muna roƙon gwamnatin mu kan ta zaƙulo masu ɗaukar nauyin ƙungiyar a fili ko a ɓoye don gurfanar da su gaban kuliya cikin hanzari.
"Ba mu yarda da baiwa tubabbun ƴan Boko Haram kariya.Matsayar ɓangaren zartarwa daban.Bazai yiwu ku ake shagwaɓa tubabbun ƴan Boko Haram ba da jindaɗi ba,su kuma wanda ayyukansu ta shafa ku barsu a sansanin ƴan gudun hijira,hakan ba adalci bane.
"Har yanzu Muna kira ga gwamnatin Najeriya da ta zaƙulo masu hannu a ɗaukar nauyin Boko Haram a zahirance ko a baɗini don yin misali akansu don ya zama izina ga masu aikata ta'addanci.I tunanin mun daɗe muna wannan kiran.
"Ban yarda da gwamnatin Najeriya ba akan sauyawa tubabbun ƴan ƙungiyar suna da kuma yafe musu laifukansu, saboda basu cancanci hakan ba.
"Ba zai yiwu ba ace kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi, su ne da laifi kuma sune da jindaɗi, inda su kuma waɗanda abin ya shafa ko oho.Na yarda cewa dani da sauran ƴan Najeriya masu yawa matsayar mu ɗaya."
Ndume ya tuno yadda wani tubabben ɗan Boko Haram yayi sanadiyyar mutuwar Kwamandan runduna ta 25 a Damboa, jihar Borno, Col. D.C Bako.
Ya ce ayyukansu basu cancanci yafiya ba sam.Ya sake tuna lokacin da aka yanka malamai 75 a ƙauyansu kaɗai yayin wani hari da ƴan ta'addan suka kai a shekarar 2015.
Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa a ranar Laraba ne sakataren gwamnatin kasar Amurka ya ce Amurka za ta taimakawa Najeriya ta fatattaki 'yan ta'adda.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng