Hukumomi 428 ba zasu iya biyan albashin watan Nuwamba ba; FG ta ankarar da ma'aikata

Hukumomi 428 ba zasu iya biyan albashin watan Nuwamba ba; FG ta ankarar da ma'aikata

- Akalla hukumomi 428 ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ba zasu iya biyan albashin watan Nuwamba ba

- Ben Akabueze, shugaban ofishin kasafi, ne ya sanar da hakan a ranar Talata yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisa

- A cewar Akabueze, karin albashin da aka yi ne bayan kammala kasafin shekarar 2019 ne dalilin faruwar hakan

Gwammatin tarayya ta ce aƙalla hukumomi 428 ne wanda ba zasu iya biyan albashin ma'aikatansu ba a ƙarshen watan Nuwamba 2020.

Shugaban ofishin kasafin kuɗi, Ben Akabueze, ne ya bayyana hakan a ranar Talata lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin Sanatoci akan asusun al'umma wato baitul mali.

Yace dalilin hakan shine an riga an gama tsara kasafin kuɗin shekarar 2019 kafin gwamnatin tarayya ta sanar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi.

Akabueze yace tuni gwamnatin tarayya ta fara shiryen sakin kuɗaɗe daga Asusun ko ta kwana na SWV (Service Wide Vote) don cike giɓin da aka samu domin biyan albashin watan Nuwamba, a cewarsa.

DUBA WANNAN: Muhimman hanyoyi 5 da mulkin Biden zai amfani Nigeria da nahiyar Afrika

Hukumomi 428 ba zasu iya biyan albashin watan Nuwamba ba; FG ta ankarar da ma'aikata
Majalisar dattijai
Asali: Facebook

Kazalika, shugaban kwamitin, Sanata Mathew Urhoghide, ya zargi ɓangaren zartarwa da rage adadin kuɗaɗen ofishin babban Oditan tarayya da gayya.

DUBA WANNAN: Tsaka mai wuya: Kotu ta gurfanar da dan majalisar APC daga arewa saboda rantsuwa a kan karya

Ya bayyana mamakinsa a fili, ganin yadda aka ragewa hukumar da aka ƙirƙira don yaƙar rashawa kuɗaɗen gudanarwa daga ɓangaren zartawa, inda kuma sauran hukumomi kamar ICPC da EFCC aka ware musu kuɗin da ya kamata.

Da yake maida bayani, Akabueze ya ce ofishin kasafin kuɗi zai tura kuɗaɗe ne ofishin babban Odita bisa tsarin da doka ta tanada idan akwai buƙatar hakan.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Ministar harkokin jinƙai da walwalar jama'a, Sadiya Farouq, ta yi iƙirarin cewa basu karɓi sisin wani daga ciki ko wajen Najeriya a matsayin tallafin yaƙi da annobar cutar COVID-19 ba.

Ministar ta bayyana hakan ne ranar Talata lokacin da take gabatar da yadda ma'aikatarta tayi amfani da kasafin kuɗinta na shekarar 2020, a gaban ƴan majalisar wakilan tarayya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel