Korona ta harbi sabbin mutane 180 a Najeriya, Bauchi da Kaduna sun yi sama

Korona ta harbi sabbin mutane 180 a Najeriya, Bauchi da Kaduna sun yi sama

- Alkaluman masu kamuwa da cutar korona a Najeriya sun dan hauhawa a 'yan kawanakin baya bayan nan

- Ana fargabar cewa annobar korona za ta sake dawowa a karo na biyu, lamarin da ya fara cusa tsoro a zukatan mutane

- Daga arewacin Najeriya, jihohin Bauchi da Kaduna sun tsallako sahun biyar na farko a teburin jihohin da aka samu sabbin masu cutar korona a ranar Laraba.

A sanarwar da ta fitar a daren ranar Litinin, cibiyar shawo kan cututtaka masu yaduwa a Najeriya (NCDC) ta ce sabbin mutane 180 sun kamu da kwayar cutar korona.

Alkaluman na ranar Litinin sun fito a gabar da ake tsoron cewa annobar korona kan iya dawowa a karo na biyu.

Sai dai, a yayin da ake fargabar cewa za'a ji jiki idan aka sake saka dokar kulle saboda dawowar korona, sai ga shi sanarwar samun rigakafin cutar ta fito daga babban kamfanin magani na Pfizer.

Jerin alkaluman mutanen da suka kamu da kwayar cutar a jihohi ya nuna jihohin Bauchi da Kaduna a mataki na hudu da na biyar.

KARANTA: Hukumomi 428 ba zasu iya biyan albashin watan Nuwamba ba; FG ta ankarar da ma'aikata

Jimillar mutane 64,516 ne aka tabbatar da cewa kwayar cutar ta kamasu a Najeriya, daga cikin adadin, an sallami mutane 60,737 bayan an tabbatar sun warke sarai.

Annobar korona ta yi sanadiyyar rasa ran mutane 1, 162 a fadin Najeriya, kamar yadda alkaluman NCDC suka nuna.

Korona ta harbi sabbin mutane 180 a Najeriya, Bauchi da Kaduna sun yi sama
Korona ta harbi sabbin mutane 180 a Najeriya, Bauchi da Kaduna sun yi sama
Asali: Twitter

Legit.ng ta rawaito cewa ministar harkokin jinƙai da walwalar jama'a, Sadiya Farouq, ta yi iƙirarin cewa basu karɓi sisin wani daga ciki ko wajen Najeriya a matsayin tallafin yaƙi da annobar cutar COVID-19 ba.

Ministar ta bayyana hakan ne ranar Talata lokacin da take gabatar da yadda ma'aikatarta tayi amfani da kasafin kuɗinta na shekarar 2020, a gaban ƴan majalisar wakilan tarayya.

KARANTA: Muhimman hanyoyi 5 da mulkin Biden zai amfani Nigeria da nahiyar Afrika

Iƙirarin ministar na zuwa ne yayin da ake tsammanin cewa ƙasa ta karɓi tallafin zunzurutun kuɗaɗen da ya tasamna biliyoyin kuɗaɗe don yakar annobar Korona.

Gudunmawar an bada ita ne don tallafawa Najeriya da ƴan ƙasar domin farfaɗowa daga gwabzar da annobar Korona ta haddasa.

A watan Afrilun shekarar 2020 haɗakar ma'aikatu masu zaman kansu na Najeriya wadanda ke yaƙi da COVID-19 (CACOVID) ta bada tallafin biliyan ₦27.160 don taimakawa a yaƙi annobar Korona da asarar da ta janyo.

Sai dai Ministar, lokacin da take jawabi, ta ce ma'aikatarta ta karɓi gudunmawar kayan abinci a matsayin tallafi, amma banda kudi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel