Annobar Corona: Ba mu karɓi ko sisi daga hannun kowa a matsayin gudunmawa ba, cewar Minista Sadiya Farouq

Annobar Corona: Ba mu karɓi ko sisi daga hannun kowa a matsayin gudunmawa ba, cewar Minista Sadiya Farouq

- Kasashe, kungiyoyi, da daidaikun mutane sun bawa gwamnati gudunmawa bayan bullar annobar korona

- Gwamnatin tarayya ta yi amfani da ma'aikatar walwala, jin kai, da bayar da tallafi wajen raba mafi yawan kayan tallafin da aka bayar gudunmmawa

- Ma'aikatar ta na karkashin jagorancin minista Sadiya Umar Farouq

Ministar harkokin jinƙai da walwalar jama'a, Sadiya Farouq, ta yi iƙirarin cewa basu karɓi sisin wani daga ciki ko wajen Najeriya a matsayin tallafin yaƙi da annobar cutar COVID-19 ba.

Ministar ta bayyana hakan ne ranar Talata lokacin da take gabatar da yadda ma'aikatarta tayi amfani da kasafin kuɗinta na shekarar 2020, a gaban ƴan majalisar wakilan tarayya.

Iƙirarin ministar na zuwa ne yayin da ake tsammanin cewa ƙasa ta karɓi tallafin zunzurutun kuɗaɗen da ya tasamna biliyoyin kuɗaɗe don yakar annobar Korona.

Gudunmawar an bada ita ne don tallafawa Najeriya da ƴan ƙasar farfaɗowa daga gwabzar da annobar Korona ta haddasa.

KARANTA: Tsaka mai wuya: Kotu ta gurfanar da dan majalisar APC daga arewa saboda rantsuwa a kan karya

A watan Afrilun shekarar 2020 haɗakar ma'aikatu masu zaman kansu na Najeriya wadanda ke yaƙi da COVID-19 (CACOVID) ta bada tallafin biliyan ₦27.160 don taimakawa a yaƙi annobar Korona da asarar da ta janyo.

Annobar Corona: Ba mu karɓi ko sisi daga hannun kowa a matsayin gudunmawa ba, cewar Minista Sadiya Farouq
Minista Sadiya Farouq @premiumtimes
Asali: Twitter

Ma'aikatar jinƙai dai itace keda alhakin sauke nauyin dukkan wasu harkokin tallafi da jinƙai a Najeriya.

Daga cikin sanannun ƴan Najeriyar da suka bada gudunmawar akwai;Aliko Ɗangote,Abdul Samad isyaka Rabi'u (BUA), Segun Agbaje (GTB), Tony Elumelu(UBA), Oba Otudeko (FBN), Jim Ovia (Bankin Zenith), Herbert Wigwe (Bankin Access) da Femi Otedola mau kamafanin raba wutar Amperion.

KARANTA: Gwamnatin tarayya ta ware Dangote daga dokar rufe iyakokin kasa

Sai dai Ministar, lokacin da take jawabi, ta ce ma'aikatarta ta karɓi gudunmawar kayan abinci a matsayin tallafi.

"Bamu karɓi ko sisi daga wata ma'aikata ko wani mutum ba a ciki da wajen Najeriya, amma mun karɓi tallafin kayan abinci", a faɗarta.

Ta kuma bayyana cewa baya ga kasafin kuɗin da gwamnatin tarayya ta warewa ma'aikatarta,babu wani agaji na musamman da ta karɓa a matsayin na COVID-19.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel