Dakarun soji sun cafke wani da ake zargi da hada kai da 'yan bindiga

Dakarun soji sun cafke wani da ake zargi da hada kai da 'yan bindiga

- Sojoji na cigaba da samun nasarori a kan 'yan bindiga da ke addabar jihohin arewa, cewar John Enenche, kakakin rundunar soji

- Enenche ya sanar da hakan a wata takarda ta ranar Litinin, inda yace Operation HADARIN DAJI sun kama wani Jamilu Usman a Funtua

- Ana zarginsa da hada kai da 'yan ta'adda, sannan sun kama wasu maza 2 a Zamfara, wadanda aka kwace miyagun makamai daga hannayensu

Rundunar Operation HADARIN DAJI da aka tura kauyen Dan-Ali, sun kama wani Jamilu Usman, wanda ake zargin ya hada kai da 'yan bindiga da ke karamar Hukumar Funtua a jihar Katsina.

Kakakin rundunar soji, Manjo Janar John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda ta ranar Litinin, inda yace yanzu haka wanda ake zargin yana hannun hukuma ana cigaba da bincike a kansa.

A cewarsa, an harbe 'yan bindiga 2 da ke ta'addanci a kauyen Fegi Baza da ke karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara, sakamakon artabun da suka yi da sojoji, inda suka samu nasarar amsar bindiga daya, mashin daya da kuma wayoyi 2.

Ya kara da cewa, rundunar Operation ACCORD sun kama wasu mutane 2 da ake zargin 'yan bindiga ne, inda aka amshi makamai iri-iri daga hannunsu, Daily Trust ta ruwaito.

Wadanda aka kama sun hada da wani Abubukar Mohammed daga karamar hukumar Bodinga da Ansi Usman Janare daga kauyen Gohono na karamar hukumar Tangaza da ke karkashin jihar Sokoto.

KU KARANTA: Bidiyo: Sojin sama sun tarwatsa ma'adanar man fetur ta 'yan ta'adda a Borno

Dakarun soji sun cafke wani da ake zargi da hada kai da 'yan bindiga
Dakarun soji sun cafke wani da ake zargi da hada kai da 'yan bindiga. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ku mayar da hankali kan matsalolin kasa ba Rahama Sadau ba - Reno Omokri

A wani labari na daban, kamfanin Pfizer da BioNTech ta ce ta samar da riga-kafin cutar korona na farko da zai iya bai wa a kalla kashi 90 na jama'a kariya daga samun cutar.

Kamar yadda The Cable ta wallafa, an gwada riga-kafin a kan mutum 43,500 a kasashe shida kuma babu wata matsala da aka samu.

Ana bada riga-kafin sau biyu amma makonni uku tsakani, kamar yadda aka gwada a Amurka, Jamus, Brazil, Argentina, South Afrika da Turkiyya. Hakan ya nuna cewa, ana samun kariya daga cutar bayan mako daya da amfani da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel