Gwamna Zulum ya karbi bakuncin Amina Mohammed a Maiduguri (hotuna)

Gwamna Zulum ya karbi bakuncin Amina Mohammed a Maiduguri (hotuna)

- Mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed ta kai ziyara jihar Borno

- Amina ta samu kyakyawar tarba daga Gwamna Babagana Umara Zulum a babbar birnin jihar, Maiduguri

- Bayan nan sun yi ganawar sirri a tsakaninsu

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya karbi bakuncin mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed a Maiduri, babbar birnin jihar.

Mohammed ta samu rakiyar manyan jami’an UN da suka hada da manyan masu bayar da shawara da kuma daraktocin majalisar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Karya ne babu wanda ya kama Rahama ko ya yanke mata hukuncin kisa, Bashir Ahmad

Gwamna Zulum ya karbi bakuncin Amina Mohammed a Maiduguri (hotuna)
Gwamna Zulum ya karbi bakuncin Amina Mohammed a Maiduguri Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Bayan nan sun yi wata ganawar sirri da gwamnan a babban masauki na filin jirgin sama ta Maiduguri.

Ga karin hotunar haduwar nasu a kasa:

KU KARANTA KUMA: Dakarun soji sun cafke wani da ake zargi da hada kai da 'yan bindiga

Gwamna Zulum ya karbi bakuncin Amina Mohammed a Maiduguri (hotuna)
Gwamna Zulum ya karbi bakuncin Amina Mohammed a Maiduguri Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Gwamna Zulum ya karbi bakuncin Amina Mohammed a Maiduguri (hotuna)
Gwamna Zulum ya karbi bakuncin Amina Mohammed a Maiduguri Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Gwamna Zulum ya karbi bakuncin Amina Mohammed a Maiduguri (hotuna)
Gwamna Zulum ya karbi bakuncin Amina Mohammed a Maiduguri Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

A wani labarin, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya jinjina wa kotun Dubai, a kan yanke wa mutane 6 masu daukar nauyin 'yan Boko Haram hukunci.

Ya yi farin cikin yadda cikin shekaru 11, aka samu hanyar gano masu daukar nauyin 'yan Boko Haram, wanda kungiyar ta yi ajalin dubbannin mutane da kuma rasa gidajen miliyoyin mutane, har da ma'aikatan gwamnatin wadanda suka kai kimar dala biliyan 9.

Duk hakan ta faru ne a jihar Borno da sauran wuraren arewa maso gabas da Najeriya gaba daya.

Sakon Zulum, wanda ya bayar a wata takarda ranar Talata, wacce kakakinsa, Malam Isa Gusau ya bayyana, ya bayar da labarin ya yadda kotun Abu Dhabi ta yanke wa wasu mutane 6 hukunci a kan tura wa kungiyar Boko Haram kusan Naira miliyan 300.

Wadanda aka yankewa hukuncin, kamar yadda ta tabbatar, sun tura dala 782,000 zuwa asusun Boko Haram a karo na 17, daga Dubai zuwa Najeriya, tsakanin 2015 zuwa 2016.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng