Karya ne babu wanda ya kama Rahama ko ya yanke mata hukuncin kisa, Bashir Ahmad

Karya ne babu wanda ya kama Rahama ko ya yanke mata hukuncin kisa, Bashir Ahmad

- Bashir Ahmad, hadimin Shugaban kasa Buhari ya yi martani a kan batun kamun Rahama Sadau

- Ahmad ya ce karya ne rundunar yan sandan Najeriya bata kama jarumar ba

- Ya kuma jadadda cewa batun cewa an yanke mata hukuncin kisa duk kanzon kurege ne

Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kafofin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ya yi watsi da rade-radin cewa rundunar yan sandan Najeriya ta kama shahararriyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau.

Bashir ya jadadda cewa duk wani labari da ke cewa an kama Rahama ko an yanke mata hukuncin kisa ba komai bane face kanzon kurege, kuma ya bukaci mutane da su yi watsi da shi.

Karya ne babu wanda ya kama Rahama ko ya yanke mata hukuncin kisa – Bashir Ahmad
Karya ne babu wanda ya kama Rahama ko ya yanke mata hukuncin kisa – Bashir Ahmad Hoto: @Rahma_sadau/@BashirAhmaad
Asali: Twitter

Ya kuma ce shi bai ga kowani kudiri mai kyau ba wajen yada labaran karya a kan jarumar kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

KU KARANTA KUMA: Na yi imani cewa mace na iya gadar Buhari, In ji Amina Mohammed

Ya ce: “Ban ga wani alfanu mai kyau ba wajen yada labaran karya game da Rahama Sadau, na fadi a baya kuma ina sake fadi a yanzu, rundunar yan sandan Najeriya bata kama Rahama ko wani ba. Duk wani labari game da kamunta ko kuma yanke mata hukuncin kisa a dauke shi a matsayin labarin karya da zuga."

KU KARANTA KUMA: Za su iya daukaka kara: FG ta yi magana a kan ma su daukan nauyin Boko Haram (da aka yankewa hukunci a UAE)

A gefe guda, wata tsohuwar 'yar wasar kwaikwayo a masana'antar Kannywood, Farida Jalal, ta bayyana cewa dakatad da Rahama Sadau da kungiyar yan wasa MOPPAN tayi ba zai canza komai ba.

A hirar da tayi da jaridar Kano Focus, Farida Jalal ta ce hakan ba zai canza irin kallon da mutane suke yiwa 'yan wasan Kannywood ba.

Ta ce wannan ba shi bane karo na farko da za'a dakatad da Rahama ba amma har yanzu babu canjin da aka samu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng