Ku cigaba da tsananta addu'a a kan masu daukar nauyin Boko Haram, Zulum

Ku cigaba da tsananta addu'a a kan masu daukar nauyin Boko Haram, Zulum

- Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya jinjina wa kotun Dubai a kan yankewa mutane 6 masu daukar nauyin Boko Haram hukunci

- An gano yadda suka yi ta tura wa 'yan Boko Haram kusan naira miliyan 300, ta hanyar canja kudin daga dala zuwa naira a karo na 17

- Dama a watan Fabrairu da Oktoba, gwamnan ya roki mutanen jiharsa da su yi azumin kwana 2 don Allah ya tona wa masu daukar nauyin Boko Haram asiri

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya jinjina wa kotun Dubai, a kan yanke wa mutane 6 masu daukar nauyin 'yan Boko Haram hukunci, Daily Trust ta wallafa.

Ya yi farin cikin yadda cikin shekaru 11, aka samu hanyar gano masu daukar nauyin 'yan Boko Haram, wanda kungiyar ta yi ajalin dubbannin mutane da kuma rasa gidajen miliyoyin mutane, har da ma'aikatan gwamnatin wadanda suka kai kimar dala biliyan 9 a jihar Borno da sauran wuraren arewa maso gabas da Najeriya gabadaya.

Sakon Zulum, wanda ya bayar a wata takarda ranar Talata, wacce kakakinsa, Malam Isa Gusau ya bayyana, ya bayar da labarin ya yadda kotun Abu Dhabi ta yanke wa wasu mutane 6 hukunci a kan tura wa kungiyar Boko Haram kusan Naira miliyan 300.

Wadanda aka yankewa hukuncin, kamar yadda ta tabbatar, sun tura dala 782,000 zuwa asusun Boko Haram a karo na 17, daga Dubai zuwa Najeriya, tsakanin 2015 zuwa 2016.

Dama gwamnan ya roki al'ummar jiharsa da su yi azumi a watan Fabrairu da Oktoban wannan shekarar, na kwana biyu, don addu'ar samun sauki a kan musibar Boko Haram.

Kuma ya roki 'yan jihar da su yi addu'ar Allah ya fallasa asirin duk wadanda suke daukar nauyin kungiyar.

KU KARANTA: Bidiyo: Sojin sama sun tarwatsa ma'adanar man fetur ta 'yan ta'adda a Borno

Ku cigaba da tsananta addu'a a kan masu daukar nauyin Boko Haram, Zulum
Ku cigaba da tsananta addu'a a kan masu daukar nauyin Boko Haram, Zulum. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Kamfanin Pfizer ya samar da riga-kafin cutar korona

A wani labari na daban, a ranar Lahadi 'yan Boko Haram sun kai hari garin Gwoza da ke jihar Borno, arewa maso gabas ta Najeriya, da tsakar dare, wanda hakan yasa sai da rundunar sojin kasa da ta sama suka yi gaggawar mayar da harin.

Karamar hukumar Gwoza tana kudu maso gabas ta Maiduguri, babban birnin jihar Borno, kuma wuri ne da 'yan ta'adda ke yawan kai wa hari. Har yanzu ba a tabbatar da irin barnar da ta faru ba sakamakon harin, jaridar HumAngle ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng