'Yan bindiga sun kai wa tawagar kwamishina hari a Zamfara

'Yan bindiga sun kai wa tawagar kwamishina hari a Zamfara

- Ƴan bindiga sun kai wa tawagar gwamnatin Jihar Zamfara hari

- Direba ɗaya daga cikin tawagar ya riga mu gidan gaskiya

- Tawagar tana dawowa ne daga Jihar Katsina inda ta tafi mika yara da mata da aka ceto da masu garkuwa

Ƴan bindiga sun afka wa tawagar gwamnatin jihar Zamfara a hanyarsu ta dawowa daga Jihar Katsina.

Tawagar ta tafi Katsina ne don mika wa gwamnatin Jihar mata da yara fiye da 26 da aka ceto daga hannun masu garkuwa.

Yan bindiga sun kai wa tawagar kwamishina hari a Zamfara
Yan bindiga sun kai wa tawagar kwamishina hari a Zamfara. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Harin Musulmin Ƙabilar Igbo: MURIC ta buƙaci a gurfanar da Rev Fr. Onah

Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu ya tabbatar da afkuwar lamarin.

"A ranar 9 ga watan Nuwamba misalin ƙarfe 10 rundunar yan sanda ta samu rahoton cewa tawagar gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin kwamishinan tsaro da ayyukan cikin gida, Alhaji Abubakar Dauran ta fuskanci barazana sakamakon musayar wuta da kungiyoyin ƴan bindiga biyu keyi a Dogon Ƙarfe, Gidan Jaja titin Zurmi - Jibiya a ƙaramar hukumar Zurmi.

KU KARANTA: Wani dan shekara 69 ya yi ikirarin ya saki matarsa don ta zabi Joe Biden a zaben Amurka

"Tawagar na dawowa daga Jihar Katsina ne bayan mika mata da yara fiye da 26 da aka sace a ƙaramar hukumar Faskari da gwamnatin Jihar Zamfara ta ceto a shirinta na sulhu da ƴan bindiga.

"Direba ɗaya daga cikin tawagar ya mutu. Nan take ƴan sanda da sojoji sun isa wurin inda suka yi wa tawagar rakiya," in ji shi.

A wani labarin daban, mutanen garin Kungurki a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a Jihar Zamfara sun daƙile harin da ƴan bindiga suka kai musu a cewar rahoton Daily Trust.

Wasu ƴan garin sun ce ƴan bindigan sun kai musu hari ne sakamakon rashin jituwa da aka samu tsakanin wani mai shago da ɗan bindiga a garin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164